Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Ziyarar Shugaban Turkiyya Erdogan Indonesia ta mayar da hankali kan ƙulla alaƙar tsaro

Shugaban Turkiyya Erdogan ya haɗu da takwaransa na Indonesia Subianto da nufin yauƙaƙa dangantaka ta ɓangaren tsaro a tsakanin ƙasashen biyu. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Indonesia Prabowo Subianto a ranar Laraba inda suka tattauna da nufin karfafa alakar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:23
Ziyarar Shugaban Turkiyya Erdogan Indonesia ta mayar da hankali kan ƙulla alaƙar tsaro
At a glance

Shugaban Turkiyya Erdogan ya haɗu da takwaransa na Indonesia Subianto da nufin yauƙaƙa dangantaka ta ɓangaren tsaro a tsakanin ƙasashen biyu. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Indonesia Prabowo Subianto a ranar Laraba inda suka tattauna da nufin karfafa alakar...

Shugaban Turkiyya Erdogan ya haɗu da takwaransa na Indonesia Subianto da nufin yauƙaƙa dangantaka ta ɓangaren tsaro a tsakanin ƙasashen biyu. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Indonesia Prabowo Subianto a ranar Laraba inda suka tattauna da nufin karfafa alakar tattalin arziki da tsaro a tsakanin kasashen biyu masu rinjayen musulmi. Kasashen biyu na gudanar da taronsu na farko na kwamitin manyan tsare-tsare na haɗin gwiwa bayan amincewa da kafa kwamitin a wani taro a Bali a shekarar 2022. "Wannan taron shi ne taro mafi girma tsakanin kasashen biyu, inda za a tattauna dukkan batutuwan da suka amfanar juna, da suka hada da muhimman batutuwa," in ji Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Indonesiya Rolliansyah Soemirat. Sanarwar da Turkiyya ta fitar ta ce tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi yanki da duniya musamman yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza. A ranar Litinin shugaban na Turkiyya ya gana da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim inda ya jaddada rashin amincewarsa da shawarar Amurka na mayar da Falasdinawa daga Gaza inda ya ce kamata ya yi Isra'ila ta biya kudin sake gina yankin. "Ba mu dauki shawarar korar Falasdinawa daga kasashen da suka shafe shekaru dubbai a matsayin wani abu da za a dauka da muhimmanci ba," in ji Erdogan. "Ba mu ɗauki shawarar da aka bayar ba ta korar Falasɗinawa daga ƙasarsu da suke zaune tsawon dubban shekaru da muhimmanci ba," in ji Erdogan.