Rundunar Sojin Turkiyya ta kawar da ƴan ta'addan PKK/YPG 11 a arewacin Syria. Rundunar Sojin Turkiyya ta “kawar da” ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda aka gano a arewacin Syria, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya ta sanar. “Ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda ke shirin kai hari kan rundunonin Olive Branch da Euphrates a arewacin Syria an kawar da su,” kamar yadda ma’aikatar ta sanar a shafinta na X a ranar Litinin. “Mun ci gaba da mayar da martani daidai gwargwado kan hare-haren ƴan ta'addan,” kamar yadda ta ƙara da cewa. Hukumomin Turkiyya suna amfani da kalmar “kawar da” domin nuna cewa ƴan ta’addan da ake magana a kai ko dai sun yi saranda ko an kashe su ko kuma an kama su. Tun daga 2016, Ankara ta yi nasarar ƙaddamar da tsare-tsare uku na yaƙi da ta’addanci a iyakokinta da ke arewacin Syria domin daƙile taruwar ƴan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan. Rundunonin sun haɗa da Euphrates Shield a 2016 da Olive Branch a 2018 da Peace Spring a 2019. A hare-haren ta'addanci da PKK ta ɗauki shekara 35 tana kaiwa a Turkiyya, Turkiyyar da Amurka da Ingila da Tarayyar Turai sun bayyanata a matsayin ta ta'addanci, ta yi ajalin sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da jarirai.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Za mu mayar da martani daidai gwargwado kan hare-haren PKK — Ma'aikatar Tsaron Turkiyya
Rundunar Sojin Turkiyya ta kawar da ƴan ta'addan PKK/YPG 11 a arewacin Syria. Rundunar Sojin Turkiyya ta “kawar da” ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda aka gano a arewacin Syria, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya ta sanar. “Ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda ke shirin kai hari kan rundunonin Oliv...

A taƙaice
Rundunar Sojin Turkiyya ta kawar da ƴan ta'addan PKK/YPG 11 a arewacin Syria. Rundunar Sojin Turkiyya ta “kawar da” ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda aka gano a arewacin Syria, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya ta sanar. “Ƴan ta’addan PKK/YPG 11 waɗanda ke shirin kai hari kan rundunonin Oliv...
