An kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotun soji Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa za ta gurfanar da wasu jami’anta a gaban kotun soji bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ta ce ya saɓa wa dokokin soji da tsarin aiki. (TRT Hausa) A wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na Hedkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar ranar Litinin, rundunar ta ce za a tuhumi sojojin da abin ya shafa kamar yadda dokar soji da sauran dokokin ƙasar suka tanada. (TRT Hausa) Sanarwar ta tunatar da cewa a watan Oktoban 2025 an kama sojoji 16 bisa zargin rashin ɗa’a da keta dokokin aiki, inda aka kammala bincike tare da miƙa rahoto ga manyan jami’ai kamar yadda doka ta buƙata. (TRT Hausa) Ta ƙara da cewa cikakken binciken da aka gudanar ya yi nazari dalla-dalla kan dukkan batutuwan da suka shafi lamarin, kuma ya gano wasu sojoji da ake zargi sun yi yunƙurin kifar da gwamnati, abin da ya saba wa ƙa’idoji da dokokin rundunar. (TRT Hausa) Rundunar ta ce duk sojojin da ake da alamar tambaya a kansu za su gurfana a gaban kotun soji domin fuskantar tuhuma, tana mai jaddada cewa za a ɗauki matakan ne bisa ƙa’ida da adalci. (TRT Hausa)
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Rundunar Sojin Nijeriya Za Ta Gurfanar da Wasu Jami’anta kan Zargin Yunƙurin Juyin Mulki
An kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotun soji Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa za ta gurfanar da wasu jami’anta a gaban kotun soji bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ta ce ya saɓa wa dokokin soji da tsarin aiki. (TRT Hausa)...

A taƙaice
An kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotun soji Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa za ta gurfanar da wasu jami’anta a gaban kotun soji bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ta ce ya saɓa wa dokokin soji da tsarin aiki. (TRT Hausa)...
