Sanarwar da hukumar CAF ta fitar ranar Alhamis ta ce za a bai wa kasar da ta lashe gasar dala miliyan bakwai, ita kuwa kasar da ta zo ta biyu za ta samu dala miliyan hudu. Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta kara kudin za ta bai wa kasar da ta lashe gasar cin kofin Afirka (AFCON) da za a yi a Côte d'Ivoire a watan Janairu. Karin ya kai kashi 40 cikin 100. Sanarwar da hukumar ta CAF ta fitar ranar Alhamis ta ce za a bai wa kasar da ta lashe gasar dala miliyan bakwai, ita kuwa kasar da ta zo ta biyu za ta samu dala miliyan hudu. Kazalika, CAF ta ce za ta bai wa kasar da zo ta uku a gasar dala miliyan biyu da rabi, yayin da kasar da ta zo ta hudu za ta samu dala miliyan daya da dubu dari uku. “Ina da kwarin gwiwar cewa, wani kaso na kudin zai yi tasiri wajen ci-gaban kwallon kafa tare da taimaka wa masu ruwa da tsaki a harkar,” kamar yadda sanarwar ta ambato shugaban hukumar CAF, Dr Patrice Motsepe, yana cewa. Ranar 13 ga watan Janairu za a fara gasar, kuma a karkare ta ranar 11 ga Fabrairu. Kasashen Afirka 24 ne za su fafata a gasar, ciki har da Nijeriya da Ghana da Kamaru da Senegal da Masar.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Za a bai wa kasar ta da lashe gasar AFCON dala milayan $7,000 000
Sanarwar da hukumar CAF ta fitar ranar Alhamis ta ce za a bai wa kasar da ta lashe gasar dala miliyan bakwai, ita kuwa kasar da ta zo ta biyu za ta samu dala miliyan hudu. Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta kara kudin za ta bai wa kasar da ta lashe gasar cin kofin Afirka (AFCON) da za a yi a...

A taƙaice