Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Za a ba da tukwuicin N10m don kama mutanen da suka kashe limamin Cocin Katolika a Enugu ta Nijeriya

Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka. Gwamnatin Jihar Enugu da ke kudancin Nijeriya ta yi alƙawarin bayar da tukwuicin naira miliyan gom...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:23
Za a ba da tukwuicin N10m don kama mutanen da suka kashe limamin Cocin Katolika a Enugu ta Nijeriya
De un vistazo

Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka. Gwamnatin Jihar Enugu da ke kudancin Nijeriya ta yi alƙawarin bayar da tukwuicin naira miliyan gom...

Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka. Gwamnatin Jihar Enugu da ke kudancin Nijeriya ta yi alƙawarin bayar da tukwuicin naira miliyan goma ga duk mutumin da ya taimaka aka kama waɗanda ake zargi da kashe fitaccen limamin cocin Katolika Matthew Eya. Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Enugu, Malachy Agbo, shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar. Wasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka. Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun yi masa kwanton-ɓauna sannan suka harbe shi a yayin da yake kan hanyar komawa gida daga Birnin Enugu Urban. Limamin cocin mamba ne na Cocin Nsukka Catholic Diocese, wadda ta tabbatar da kisansa.