Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Za a ƙaddamar da Tashar TRT ta Spaniyanci a wajen Babban Taron Yaɗa Larabarai na Spaniya a Istanbul

Babban Taron na da manufar ɗabbaka tattaunawar al'adu daban-daban da haɗa kai tsakanin kasashen da ke magana da harshen Spaniyanci, tare da haskaka rawar da Turkiyya ke takawa wajen zama gada a tsakanin al'adu mabambanta. Kafar yada labarai ta Turkiyya, TRT, a karon farko za ta karɓi baƙuncin Bab...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:23
Za a ƙaddamar da Tashar TRT ta Spaniyanci a wajen Babban Taron Yaɗa Larabarai na Spaniya a Istanbul
Bu haberde ne var?

Babban Taron na da manufar ɗabbaka tattaunawar al'adu daban-daban da haɗa kai tsakanin kasashen da ke magana da harshen Spaniyanci, tare da haskaka rawar da Turkiyya ke takawa wajen zama gada a tsakanin al'adu mabambanta. Kafar yada labarai ta Turkiyya, TRT, a karon farko za ta karɓi baƙuncin Bab...

Babban Taron na da manufar ɗabbaka tattaunawar al'adu daban-daban da haɗa kai tsakanin kasashen da ke magana da harshen Spaniyanci, tare da haskaka rawar da Turkiyya ke takawa wajen zama gada a tsakanin al'adu mabambanta. Kafar yada labarai ta Turkiyya, TRT, a karon farko za ta karɓi baƙuncin Babban Taron Kasashen da ke Magana da Yaren Spaniyanci da ƙaddamar da kafar TRT Espanol (Spaniyanci) a Istanbul a ranakun 25 da 26 ga Afrilu, da manufar haɓaka muryar ƙasar a duniya. Babban Taron zai kuma gabatar da ƙaddamar da tashar TRT Espanol (Sashen Hausa na TRT Spaniyanci), da zai fara gabatar da shirye-shirye a shafukan sada zumunta da yanar gizo a hukumance. Mahalarta Taron sun hada da Janaral Manaja 17 da 'yan jarida 21 da shugabannin zartarwa 16 daga kasashe 18 da ke magana da harshe Spaniyanci irin su Spaniya da Mexico da Colombia da Ajantina da Peru da Venezuela da Guatemala da Ecuador da Bolovia. Dadin dadawa, Daliban 40 daga Latin Amurka da Spaniya da ke karatu a Turkiyya z asu halarci taron. Taron zai fara da taron horarwa ga 'yan jaridu daga kasashen da ke magana da yaren Spaniyanci a ranar 25 ga Afrilu. Taken bayar da horon shi ne "Aikin Jarida na Kasa da Kasa", kuma zai mayar da hankali kan batutuwa irin su aikin jarida na gaskiya, abubuwan da jama'a suke tsammani, alakar kasa da kasa, da tasirin siyasa ga kafafen yada labarai, da kuma musayar ra'ayoyi. Batutuwan muhawara a wajen taron A ranar 26 ga Afrilu, za a kaddamar da sabuwar tashar ta yanar gizo, TRT Spaniyanci. Za a bude taron da fara gudanar da jawabin bude taro daga Daraktan Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Fahrettin Altun, da Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci. Bayan ƙaddamar da TRT Spaniyanci, da rana kuma za a gudanar da tarukan muhawara da tattaunawa tare da ƙwararrun mahalarta. Batutuwan da za a tattauna a zaman muhawarorin sun hada da: "Karfafa Fahimtar Juna Ta Hanyar FIna-Finai Masu Dogon Zango: Turkiyya da Kasashen da ke magana da Yaren Spaniyanci," "Alakar Turkiyya da Kasashen da ke magana da Yaren Spaniyanci ta Fuskar Kafafan Yada Labarai: Manufar Bai-Daya da Kabulabale a Nan Gaba," da kuma "Sauyawar Samun Labarai a Duniya: Habaka Muryoyin Kasashe masu magana da Yaren Spaniyanci don Fahimtar Duniya da Adalci." Hade bangarorin al'adu A karkashin taken "Wajen da Mutane ke da Daraja," TRT Spaniyanci na da manufar hade bangarorin al'adu biyu waje guda ta hanyar gabatar da ingantattun labarai da wakiltar abubuwan da ke afkuwa a duniya da mahanga ta musamman. Za ta bayar da labarai da shirye-shirye na musamman ga masu magana da yaren Spaniyanci, yaren da ake magana da shi a kasashe sama da 20 a duniya. Haka zalika, za ta dinga kawo labaran da suka shafi jama'ar da ke magana da yaren Spaniyanci, harshen da ake magana da shi a kasashe sama da 20 a duniya. Sannan kuma, shafukan sada zumuntar zai tattara kusan mutane rabin biliyan a waje guda, yana haskaka mabambantan al'adu, fasaha da basira, da yalwa ta hanyar gabatar da labarai na musamman. Wannan babbar murya za ta yi amo daga Turkiyya zuwa Latin Amurka.