Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Yankin Kerala na India na fama da wata cuta da ke cinye ƙwaƙwalwa

Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi. Mutane 19 sun mutu a jihar kudancin India ta Kerala a 2025 sakamakon kamuwa da cutar ‘amoebic meningoencephalitis’ (PAM) mai cinye ƙwaƙwalwa, in ji Kwamishin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:23
Yankin Kerala na India na fama da wata cuta da ke cinye ƙwaƙwalwa
Kwa muhtasari

Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi. Mutane 19 sun mutu a jihar kudancin India ta Kerala a 2025 sakamakon kamuwa da cutar ‘amoebic meningoencephalitis’ (PAM) mai cinye ƙwaƙwalwa, in ji Kwamishin...

Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi. Mutane 19 sun mutu a jihar kudancin India ta Kerala a 2025 sakamakon kamuwa da cutar ‘amoebic meningoencephalitis’ (PAM) mai cinye ƙwaƙwalwa, in ji Kwamishinar Lafiya ta jihar Veena George. George ta ce jimillar mutane 69 ne suka kamu da cutar a wannan shekarar. Jihar ta bayar da sanarwar kar ta kwana a yayin da cutar ke yaduwa, tashar talabijin din jihar DD ta rawaito hakan. Ana kamuwa da cutar ‘Naegleria fowleri’ da ba a saba gani ba a wuraren ninkaya marasa tsafta, wuraren wasan ruwa da sauran wuraren nishadi, in ji Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka CDC. Ana yawan kiran cutar da ‘Amoeba mai cinye kwakwalwa” saboda tana iya kama kwakwalwar tare da lalata jijiyoyi da fatar ƙwaƙwalwar, kamar yadda aka bayyana a shafin intanet na CDC.