Matashin ɗanwasan ya ce filin zai zama wajen “rubuta tarihi” Yayin da Barcelona ke shirin komawa filin wasanta na Camp Nou, tauraron ƙungiyar, Lamine Yamal, ya aika saƙo na musamman ga masoyansa. Yamal, mai shekara 18, ya sha alwashin cewa zai jagoranci Barcelona wajen kafa tarihin nasarori a filin wasan, wanda za a koma buga wasa a ƙarshen mako bayan an kammala wasu gyare-gyare. Filin Camp Nou ya kasance a rufe kusan kwanaki 900 saboda gyare-gyaren da suka janyo Barcelona ta daina buga wasa a ciki, duk da cewa wasu gyare-gyare ba a kammala su ba har yanzu. Matashin ɗanwasan ya bayyana cewa dawowa Camp Nou zai zama abin farin ciki a gare shi, musamman bayan ya bar tawagar ƙasarsa, Sifaniya, don jinyar cutar matsematsi da yake fama da ita. A satin nan, Yamal ya wallafa hotunan filin a shafinsa na Instagram, gabanin wasan Barcelona da Athletic ranar Asabar, 22 ga Nuwamba. A saƙonsa, ya rubuta: “Camp Nou ne wajen da za a rubuta tarihi.” Tun daga watan Mayu 2023, Barcelona ta rika buga wasanni a filin Lluis Companys Olympic Stadium a Montjuic. A farkon Nuwamba aka yi nasarar gwajin atisaye inda ‘yan-kallo 23,000 suka samu shiga, yayin da yanzu aka ba izinin shigar da ‘yan-kallo 45,401. Tushen labari: Newstimehub
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Lamine Yamal ya yi alkawarin jagorantar Barcelona dawowa Camp Nou
Matashin ɗanwasan ya ce filin zai zama wajen “rubuta tarihi” Yayin da Barcelona ke shirin komawa filin wasanta na Camp Nou, tauraron ƙungiyar, Lamine Yamal, ya aika saƙo na musamman ga masoyansa. Yamal, mai shekara 18, ya sha alwashin cewa zai jagoranci Barcelona wajen kafa tarihin nasarori a fil...

A taƙaice
Matashin ɗanwasan ya ce filin zai zama wajen “rubuta tarihi” Yayin da Barcelona ke shirin komawa filin wasanta na Camp Nou, tauraron ƙungiyar, Lamine Yamal, ya aika saƙo na musamman ga masoyansa. Yamal, mai shekara 18, ya sha alwashin cewa zai jagoranci Barcelona wajen kafa tarihin nasarori a fil...
