Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Yakin Gaza na fadada zuwa wani abu daban: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan

A yayin wani taron hadin gwiwa na 'yan jarida da ya gudanar da takwaransa na Kuroshiya, babban jami'in diflomasiyya na Turkiyya ya bukaci kasashen duniya da kar su kawar da kawunansu daga alamun ta'azzarar rikicin a Tekun Maliya da Siriya da Iraki. Al'amuran da ke afkuwa a Gabas ta Tsakiya na nun...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:23
Yakin Gaza na fadada zuwa wani abu daban: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan
De un vistazo

A yayin wani taron hadin gwiwa na 'yan jarida da ya gudanar da takwaransa na Kuroshiya, babban jami'in diflomasiyya na Turkiyya ya bukaci kasashen duniya da kar su kawar da kawunansu daga alamun ta'azzarar rikicin a Tekun Maliya da Siriya da Iraki. Al'amuran da ke afkuwa a Gabas ta Tsakiya na nun...

A yayin wani taron hadin gwiwa na 'yan jarida da ya gudanar da takwaransa na Kuroshiya, babban jami'in diflomasiyya na Turkiyya ya bukaci kasashen duniya da kar su kawar da kawunansu daga alamun ta'azzarar rikicin a Tekun Maliya da Siriya da Iraki. Al'amuran da ke afkuwa a Gabas ta Tsakiya na nuni da yadda yakin Gaza da ya dauki tsawon watanni uku ke sauyawa zuwa wani abu mai fadi na daban, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan. "Kar ya zama wani abu mai rikitarwa cewa a ga abin da ya afku a Tekun Maliya, Syria da Iraki zai sauya fasali daga tokar rikicin Gaza zuwa wani sabon rikici babba," Fidan ya fada wa taron 'yan jaridu a ranar Talata da ya gabatar da takwaransa na Kuroshiya Gordan Grlic-Radman a babban birnin Ankara. Fidan ya kara da cewa Turkyya a lokuta daban-daban ta sha nanata ba za taba samun dauwamammen zaman lafiya ba a yankin har sai samar da tsaro da 'yancin cin gashin kan kasar Falasdinawa. Isra'ila ta kai hare-hare ba kakkautawa ta sa da kasa kan Gaza tun bayan harin kan iyaka da Hamas ta kai musu inda Tel Aviv ke cewa mutane 1,200 aka kashe. A kalla Falasdinawa 24,285 mafi yawan su mata da yara kanana, inda aka jikkata wasu 61,154, kamar yadda mahukuntan Falasdinawa suka bayyana. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an raba kaso 85 na jama'ar Gaza da matsugunansu, a yayin da suke tsaka da matsanancin rashin abinci, tsaftataccen ruwan sha da magunguna, kuma an rusa kaso 60 cikin dari na gine-ginen yankin. Kawancen Turkiyya da Kuroshiya Bayan gana wa da takwarans ana Kuroshiya, babban jami'in diplomasiyyar Turkiyya Fidan ya zayyana muhimmancin ci gaba da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Balkan don amfanin Turkiyya da Kuroshiya, musamman wajen goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali da kare martabatar iyakokin Bosnia da Herzegovina. Da yake bayar da misali ga ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kai zuwa Zagreb shekaru biyu da suka gabata, Fidan ya jaddada cewa ziyarar ta habaka alakarsu, kuma a yayin wannan ziyara ta Grlic-Radman a yanzu haka, an tattauna kan hanyoyin da za a hada kai da kara karfafa dangantakar. Ya kuma yi karin haske kan ayyuka tare don karfafa alaka a dukkan bangarori, kuma akwai yarjeniyoyi da ake kulla alaka a kansu, yana mai fatan cewa za su sanya hannu a kan nan da wani dan lokaci. Game da alakar tattalin arziki da kasuwanci, Fidan ya bayyana cewa suna da burin habaka jarin kasuwanci da ke tsakaninsu ya kai na dala biliyan biyu, ya kuma jaddada muhimmancin da ke tattare da habaka amfani da dabarun hukumomin gwamnati yadda ya kamata, ciki har da Hukumar Tattalin Arziki ta Hadin Gwiwa. Da yake bayyana gamsuwa da yadda kamfanonin Turkiyya ke kara nuna sha'awa ga Kuroshiya, musamman a bangaren yawon bude ido da gine-gine da sufuri da harkokin banki, da makamashi mai sabuntuwa, ya lura da cewa ana maraba da zuba jarin 'yan kasar Kuroshiya a Turkiyya. Fidan ya yi karin haske kan muhimmancin majalisar tuntubar juna ta kasashe uku na Turkiyya, Bosnia da Herzegovina da Kuroshiya, yana mai bayyana zakuwarsu na sake gudanar da taro na gaba. 'Turkiyya za ta kasance babbar kawar Tarayyar Turai' A yayin taron 'yan jaridun na hadin gwiwa, Ministan Harkokin Wajen Kuroshiya da harkokin Tarayyar Turai Gordan Grlic-Radman ya ambaci sun tattauna kan alakar Turkiyya da Tarayyar Turai tare da Minista Fidan, kuma ya ce Turkiyya na kan matsayin neman zama mamban Tarayyar. "A wajenmu, Turkiyya mai neman shigaba Tarayyar Turai ce kuma za ta kasnace babbar kawar Tarayyar," in ji shi, yana mai jaddada cewa suna ci gaba da tattaunawa don habaka kyakkyawan yanayi tsakanin Tarayyar Turai da Turkiyya. Da yake bayyana gamsuwarsa kan ziyarar da shugaba Erdogan ya kai ta karshe zuwa Kuroshiya, Radman ya yi nuni kyakkyawan tasirin da take da shi, wanda ya bayar da damar sanya hannu kan yarjeniyoyi uku, da tabbatar da yarjejeniyar diflomasiyyar da aka faro shekaru 32 da suka gabata, inda ya zuwa yanzu kasashen suka sanya hannu kan yarjeniyoyi 50. Ya bayyana godiyarsa ga zuba jarin da 'yan kasuwar Turkiyya suka yi a Kuroshiya, tare da cewar ana kaunar su sosai a kasar. Ya kuma gode wa Turkiyya bisa goyon bayan da take bayarwa ta hanyar Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki da Cigaba (ECDO). Da yake tabo batun kawancen NATO da rawar da kasashen biyu ke takawa a Turai, Radman ya jaddada muhimmancin habaka wa da aiki da Kungiyar Kasashe Ukun.