Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kai hare-hare fiye da 2,970 a shekarar 2024 a kan Falasɗinawa da dukiyoyinsu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye. Wasu Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun ƙona wani masallaci a arewa maso yammacin birnin Jericho da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a ranar Lahadi, kamar yadda wani ɗan gwagwarmaya a yankin ya tabbatar. Hasan Mleihat na kungiyar kare hakkin Larabawa makiyaya ya shaoda cewa Yahudawan sun kuma ƙona wata tarakata a cikin al’ummar Mleihat Bedouin. “Sun ƙona masallacin baki ɗaya, sai dai mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kashe wutar da ta kama a tarakatar,” kamar yadda ya ƙara da cewa. Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kai hare-hare fiye da 2,970 a shekarar 2024 a kan Falasɗinawa da dukiyoyinsu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda alƙaluman Falasɗinu suka nuna. Aƙalla Falasɗinawa 10 aka kashe tare da lalata bishiyoyin zaitun 14,000 a yayin harin. Kimanin Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna 770,000 ne ke zaune a wurare 180 da suka mamaye a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun ƙona wani masallaci na Falasɗinawa
Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kai hare-hare fiye da 2,970 a shekarar 2024 a kan Falasɗinawa da dukiyoyinsu a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye. Wasu Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun ƙona wani masallaci a arewa maso yammacin birnin Jericho da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a r...