Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Yadda zanga-zangar ɗalibai ke neman durƙusar da jami'o'in Amurka

Ɗumbin ɗalibai daga jami'o'in Amurka da dama ne ke zanga-zanga inda ɗaliban ke kira ga jami’o’insu su yanke hulɗa da kamfanonin da ke da alaƙa da Isra’ila, inda a wasu jami’o’in ma, ana kira kan jami’o’in su yanke hulɗa da Isra’ilar baki ɗaya. Guguwar zanga-zangar ɗalibai ta taso a Amurka inda ak...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:23
Yadda zanga-zangar ɗalibai ke neman durƙusar da jami'o'in Amurka
A taƙaice

Ɗumbin ɗalibai daga jami'o'in Amurka da dama ne ke zanga-zanga inda ɗaliban ke kira ga jami’o’insu su yanke hulɗa da kamfanonin da ke da alaƙa da Isra’ila, inda a wasu jami’o’in ma, ana kira kan jami’o’in su yanke hulɗa da Isra’ilar baki ɗaya. Guguwar zanga-zangar ɗalibai ta taso a Amurka inda ak...

Ɗumbin ɗalibai daga jami'o'in Amurka da dama ne ke zanga-zanga inda ɗaliban ke kira ga jami’o’insu su yanke hulɗa da kamfanonin da ke da alaƙa da Isra’ila, inda a wasu jami’o’in ma, ana kira kan jami’o’in su yanke hulɗa da Isra’ilar baki ɗaya. Guguwar zanga-zangar ɗalibai ta taso a Amurka inda ake yinta a jami’o’i da dama na Amurka inda ɗaliban ke kira ga jami’o’insu su yanke hulɗa da kamfanonin da ke da alaƙa da Isra’ila, inda a wasu jami’o’in ma, ana kira kan jami’o’in su yanke hulɗa da Isra’ilar baki ɗaya. Zanga-zangar ɗaliban wadda rabon da a ga irin ta tun wadda aka yi a ƙasar a jami’o’i a lokacin yaƙin Vietnam tsakanin shekarun 1960 zuwa 1970 – wadda ta jawo aka kama ɗaruruwan ɗalibai. Jami’ai na ƙoƙarin daƙile wannan zanga-zanga a daidai lokacin da ake shirin kawo ƙarshen zangon karatu na ƙarshe a jami’o’i. Ga bayanai na baya-bayan nan dangane da zanga-zangar da ake yi a jami’o’in Amurka Jami’ar Columbia Jami'an 'yan sandan birnin New York da dama sun shiga Jami'ar Columbia tare da kame masu zanga-zangar, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito, yayin da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da ke wajen harabar jami'ar suka yi wa 'yan sanda masu dauke da makamai ba'a. ‘Yan sandan sun saka kimanin mutum 50 waɗanda suka kama cikin wata motar bas, kowannen su an daure hannuwansu a bayansu da igiya, duk wurin ya haskaka da fitulun motocin ‘yan sanda masu haske da ja da shudi. Motocin daukar marasa lafiya da sauran motocin agajin gaggawa sun tsaya wurin. Shortly before officers entered the campus, the New York Police Department received a notice from Columbia authorising officers to take action, a law enforcement official told The Associated Press. The university's president, Minouche Shafik, asked the police to remain on campus until May 17. The police deployment came after the university threatened protesters with expulsion. Jim kadan kafin jami’an su shiga harabar jami’ar, ‘yan sandan New York sun samu sanarwa daga Columbia da ke ba jami’an izinin daukar mataki, kamar yadda wani jami’in tsaro ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press. Shugaban jami’ar, Minouche Shafik, ya bukaci ‘yan sanda da su ci gaba da zama a harabar har zuwa ranar 17 ga watan Mayu. Rundunar ‘yan sandan ta zo ne bayan jami’ar ta yi barazanar korar masu zanga-zangar. Jami'an NYPD sun yi jigilar daliban da aka kama a cikin wata motar safa yayin da suke kokarin fitar da mutane daga wani gini da masu zanga-zangar neman goyon bayan Falasdinu suka yi a jami'ar Columbia. Brown University has reached an agreement with students protesting against Israel's war on Gaza to end an encampment they have been maintaining on school grounds since April 24 in solidarity with Palestinians. "Students agreed to end the encampment and refrain from further actions that would violate Brown's conduct code through the end of the academic year," Brown University said in a statement. The university, located in Providence, Rhode Island, said although the establishment of tents and other activities have violated a range of policies, the university leaders agreed that ending the encampment will be viewed favourably in disciplinary proceedings. Jami'ar Brown Jami'ar Brown ta cimma yarjejeniya da daliban da ke zanga-zangar adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza domin kawo karshen zaman dirshen ɗin da suke ci gaba da yi a harabar makaranta tun ranar 24 ga watan Afrilu domin nuna goyon baya ga Falasdinawa. "Dalibai sun amince da kawo karshen zaman dirshen tare da guje wa wasu ayyuka da za su keta ka'idojin ɗa'ar Jami'ar Brown a karshen shekarar karatu," in ji Jami'ar Brown a cikin wata sanarwa. Jami'ar ta amince da cewa za a gayyaci dalibai biyar don ganawa da mambobi biyar na Jami'ar Brown a watan Mayu don sauraron hujjojinsu kan dalilin da zai sa jami'ar ta janye daga Isra'ila. "Bugu da ƙari, [Shugabar Jami'ar Brown Christina] Paxson za ta nemi Kwamitin Ba da Shawarwari kan Gudanawa na Jami'ar da ya ba da shawara game da batun yanke alaƙa zuwa ranar 30 ga Satumba,inda ake sa ran jami'ar za ta kaɗa kuri'a a taronta na Oktobar 2024. " a cewar jami'ar.