Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Yadda yaƙi ya lalata tattalin arziƙin Sudan

Tattalin arzikin Sudan da a baya yake da ƙarfi a halin yanzu ya lalace, inda yaƙi ya raba miliyoyin jama'a da muhallansu, da lalata ababen more rayuwa, da jefa kasar cikin yunwa. Kafin sojojin Sudan da rundunar RSF su soma rikici da juna a bara, Ahmed ya kasance mai sayar da ɗaya daga cikin manya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:23
Yadda yaƙi ya lalata tattalin arziƙin Sudan
At a glance

Tattalin arzikin Sudan da a baya yake da ƙarfi a halin yanzu ya lalace, inda yaƙi ya raba miliyoyin jama'a da muhallansu, da lalata ababen more rayuwa, da jefa kasar cikin yunwa. Kafin sojojin Sudan da rundunar RSF su soma rikici da juna a bara, Ahmed ya kasance mai sayar da ɗaya daga cikin manya...

Tattalin arzikin Sudan da a baya yake da ƙarfi a halin yanzu ya lalace, inda yaƙi ya raba miliyoyin jama'a da muhallansu, da lalata ababen more rayuwa, da jefa kasar cikin yunwa. Kafin sojojin Sudan da rundunar RSF su soma rikici da juna a bara, Ahmed ya kasance mai sayar da ɗaya daga cikin manyan abubuwan da Sudan ke fitarwa: wato ƙaro, wanda yana da muhimmanci ga tattalin arziƙin ƙasar. A halin yanzu ba shi da sana'a, kuma labarinsa ya nuna yadda tattalin arziƙin Sudan ya taɓarɓare sakamakon yaƙin da aka shafe watanni goma ana gwabzawa. Tun bayan da aka soma rikici tsakanin janarorin biyu masu adawa da juna a ranar 15 ga watan Afrilu, Ahmed ya kasance cikin wahala. "A lokacin da aka soma yaƙin, inda da tarin ƙaro a cikin ɗakin ajiyata a kudancin Khartoum wanda na yi niyyar fitarwa," kamar yadda Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP inda ya buƙaci a yi amfani da sunansa na farko kaɗai domin gudun kada a mayar masa da martani. "Domin fitar da shi waje, sai da na biya kuɗi masu yawa ga rundunar RSF," wadda ita ce rundunar da ke ƙarƙashin Mohamed Hamdan Daglo waɗanda ke yaƙi da sojojin Sudan ƙarƙashin Abdel Fattah al-Burhan. "Sai da na biya kuɗi masu yawa a wuraren da ke ƙarƙashin ikonsu kafin kayayyakina su kai wuraren da gwamnati ce ke da iko da su," kamar yadda Ahmed ya bayyana. Sai dai gwamnatin wadda ke biyayya ga sojojin ƙasar "ta nemi na biya haraji" kan kayayyakin, wanda ake amfani da shi wurin yin abubuwa da dama da ga ciki har da lemo da cingam. A lokacin da manyan motocin ɗaukar kayan suka isa Port Sudan don fitar da su a tekun Bahar Maliya, "hukumomi sun sake neman a biya kuɗin haraji, kuma sai da na biya kudin ajiya sau shida fiye da kafin yakin", in ji Ahmed. Ƙaronsa, kamar sauran kayayyakin Laranawa da dama bai hau kan jirgin ruwa ba. Kamar yadda hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Sudan ta bayyana, cinikayyar ƙasa da ƙasa ta ragu da kashi 23 cikin 100. Shafe gomman shekaru kafin a farfaɗo Ma'aikatar kuɗi ta ƙasar wadda ba ta yi kasafin kuɗi na shekarar 2023 da 2024 ba ta ƙara kuɗin shigo da kayayyaki daga fam 650 na Sudan zuwa 950. Amma har yanzu hakan ya yi ƙasa da ainihin ƙimar kuɗin. Yayin da akasarin bankunan ba su aiki, farashin musaya daya tilo da ya shafi talakawan Sudan shi ne a kasuwar bayan fage, inda a halin yanzu dala ke kan kusan fam 1,200 na Sudan. "Wannan wata alama ce ta lalacewar tattalin arziƙin Sudan," kamar yadda tsohon shugaban hukumar kasuwanci da cinikayya ta Sudan al-Sadiq Jalal ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP. Babban abin da ya fi muni, katsewar hanyoyin sadarwa tun farkon watan Fabrairu ya kawo cikas ga hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo - wacce 'yan Sudan suka dogara da ita don tsira. Yakin ya sa masana'antu sun daina samar da kayayyaki. Wasu kuma an lalata su. An wawashe kayayyakin abinci daga shaguna. Bankin Duniya a watan Satumba ya ce "irin ɓarnar da aka yi wa tushen tattalin arzikin Sudan ya mayar da ci gaban kasar baya da shekaru da dama" kamar yadda ya bayyana. Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya yi hasashem cewa k oda bayan yaƙin, "ƙasar za ta shafe shekaru tana sake gina kanta".