Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Yadda kadaici ke gusar da farin ciki da yi wa mutane kisan mummuke

Kaɗaici da keɓance kai a cikin al'umma na zuwa da babban hatsarin mutuwa da wuri, sama da hatsarin da shan taba sigari da yawan shan giya ko mummunar ƙiba ke janyowa, in ji WHO a wani gargaɗi da ta fitar. Daga Sylvia Chebet Alkaluman da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO (WHO) ta fitar sun nuna...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:23
Yadda kadaici ke gusar da farin ciki da yi wa mutane kisan mummuke
En bref

Kaɗaici da keɓance kai a cikin al'umma na zuwa da babban hatsarin mutuwa da wuri, sama da hatsarin da shan taba sigari da yawan shan giya ko mummunar ƙiba ke janyowa, in ji WHO a wani gargaɗi da ta fitar. Daga Sylvia Chebet Alkaluman da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO (WHO) ta fitar sun nuna...

Kaɗaici da keɓance kai a cikin al'umma na zuwa da babban hatsarin mutuwa da wuri, sama da hatsarin da shan taba sigari da yawan shan giya ko mummunar ƙiba ke janyowa, in ji WHO a wani gargaɗi da ta fitar. Daga Sylvia Chebet Alkaluman da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO (WHO) ta fitar sun nuna cewa wata annoba na kashe jama a sirrance, cikin sauri kuma ba tare da bambance shekarunsu ba. Kadaici da keɓe kai daga jama'a sun zama musabbabin mutuwa da yawa. "Kadaici na shafar lafiya da walwalar mutum sosai," in ji Alana Officer, shugabar sashen sauyin yanayin jama'a da kula da lafiyar tsofaffi na WHO, yayin tattaunawar da TRT Afirka. "Shaidar da ake da ita a hannu ta bayyana rashin kusantar jama'a da mu'amala da su na kashe mutane sosai, sama da wasu cututtuka da aka san su da kashe ɗan'adam irin shan taba, yawan shan giya, rashin motsa jiki, kiba da gurbacewar iska." Kwararru na cewa kaɗaici, na zahiri ko na baɗini, na ƙara yiwuwar fuskantar hatsarin kashe kai da mutuwar barin jiki da damuwa da cutar mantuwa da ƙunar zuci da ma wasu da dama. WHO ta ce hakan na ta'azzara yiwuwar kamuwa da ciwon zuciya da kaso 30. Batutuwa daban-daban WHO ta bayar da ma'anar kebance kai daga jama'a da rashin samun cudanya da mutane yadda ya kamata, kadaici kuma a matsayin jin ciwon zuci sakamakon rashin mu'amala da mutane. Yi tunani kai kadai a cikin taron jama'a. da yawa daga cikin mu na iya fuskantar wannan matsala. Sabanin fahimtar da aka yi ta cewa tsofaffin mutane a kasashen Yamma na shan wahala saboda kebe kai daga jama'a da kadaici, wannan yanayi na shafar mutane a dukkan matakin shekaru a duniya. "Kimanin kaso 25 na tsofaffin mutane na fuskantar matsalar kebe kai da kadaici, inda kaso 5 zuwa 15 na matasa suka kebantu daga cikin jama'a," in ji Alana, tana rawaito sakamakon binciken WHO. Daya daga cikin tsofaffi hudu a duniya na fuskantar kadaici da kebantuwa daga jama'a.. Hoto: Reuters Akwai yiwuwar a ki bayar da muhimmanci ga wadannan alkaluma da ke sanya damuw ada Hukumar MDD ta fitar. Duk da haka suna bayar da haske game da tsananin damuwa kan lafiyar jama'a, wana ke bukatar kulawar gaggawa. Alana ta yi gargadi da cewa "Mutane da dama na fuskantar kadaici, wanda na iya cutarwa sosai." Hukumar kula da mu'amala da jama'a WHO ta kafa wata sabuwar hukuma kan mu'amala da jama'a don magance matsalar kadaici da ta zama babbar barazana ga lafiya, hukumar na da alhakin inganta cudanya da mutane a matsayin abu da ke bukatar fifiko, da kuma samar da hanyoyin mafi kyau da inganci wajen magance matsalar. Hukumar na da shekaru uku na gabatar da aikinta, wanda a wannan wa'adi za ta bayar da haske kan yadda mu'amala da jama'a yake inganta lafiyar al'ummu da jamaa, kuma na taimakawa wajen cigaban tattalin arziki, zamantakewa da karfafa basira. Alana ta shaida wa TRT Afirka cewa "Ina fatan ta hanyar ayyukan wannan hukuma, mutane za su fahimci cewa suna fuskantar kadaici da kebantuwa daga jama'a, sannan su gano meye ya kamata mu yi don magance matsalar." Alamun kebance kai daga jama'a Kwararru sun lura da cewa mutum na iya zama mai jama'a, yana da aure ko rayuwa a gidan da ya hada mutane da yawa, amma duk da haka sai ya zama shi kadai. "Wannan dabara ta mu'amala da jama'a ta ta'allaka ga yadda kake mu'amala ko kusantar wasu mutanen daban, ko a wajen aikinka, a makota ko cikin al'umma," in ji Alana. A yayin da mutane suka gaza samun tallafi a lokacin da ake bukata, suna iya zama an kebe su daga sauran jama'a. A yayin da mutum ya gaza samun taimakon da ya kamata a zahiri ko badini, sai su ji sun zama su kadai ko an kebe su daga jama'a. Hoto: Getty Image Alana ta ce wannan na faruwa ne a lokacin da taimakon zahiri ko a badini da mutum ya kamata ya samu ya zama kadan ko ta'azzara. "Ba lalai ne su zama sun wadatar da kai ka ji cewa kana tare da mutane, al'ummar unguwa ko na gari ba." Tasirin zamantakewa da tattalin arziki Idan aka kalli lamarin a bude, duk wani da zai iya tafiya da farin cikin mutane, to zai iya janyo sakamakon tattalin arziki mara kyau. Idan mutum yana wani aiki kuma yake jin ba ya tare da kowa, hakan na karya masa zuciya da janyo rashin samun sakamako mai kyau da gamsuwa da aikin. Barin aiki ko korar mutum da aiki na iya yiwuwa sakamakon wadannan matsaloli ne. "A yayin da ka fahimci cewa ba ka cikin farin ciki, ba ka jin dadin yadda kake mu'amala da sauran mutane, to yana da muhimmanci ka yi wani abu game da haka," Alana ta bayar da shawara inda ta kara da cewa a wasu lokutan hakan na da matukar wahalar zartarwa. A wani sako da shugaban WHO Tedros Adhanom ya fitar ta shafin X ya bayyana irin kalubale da hatsarin da ke tattare da kadaici. Ya ce "Akwai bukatara mu tattauna kan wannan a bayyane. Ba matsala ba ne ka samu kwararru." Loneliness can have a serious impact on our health and well-being — it increases the risk of early death and developing dementia, stroke and cardiovascular diseases. We need to talk more openly about it. It's OK to reach out. Thank you @jogumanstudio for working together with… https://t.co/j5wZJpqVE1 — Tedros Adhanom Ghebreyesus (@DrTedros) November 16, 2023 A tsakanin matasa, rashin cudanya da jama'a na iya janyo rashin kwazo a makaranta. WHO na cewa alkaluma sun nuna matasa da ke fuskantar kadaici a makarantun sakandire ne aka fi yawan kora a jami'a. Jakadan matasa na Tarayyar Afirka, Chido Mpemba, kuma daya daga shugaban Tarayyar ya lura da cewa "A Afirka da ma wajen ta, dole ne mu sake fasalin yadda ake tattaunawa da kula da kadaici. Zuba jari a mu'amalar jama'a na da muhimmanci wajen samar da al'umma mai amfani da nagarta, samar da tattalin arziki mai karfi da zai habaka jn dadin al'ummar yau da na gobe." Karfin mu'amala da jama'a WHO ta kafa hukuma don taimakawa wajen inganta mu'amalar jama'a a matsayin abun baiwa fifiko a kula da lafiya a duniya.. Hoto: Ghetty Images. A matakin daidaikun mutane, Alana ta ce zai iya taimakawa a ce ka nemi taimakon wani ko wasu wajen ganawa, misalin kira a wayar tarho. "Maimakon aika sako ga wani, ka kira su a waya," in ji ta. Wasu hanyoyin magance matsalar sun hada da karar da ingantaccen lokacin mutum tare da iyali da abokai. Alana ta kuma karfafi gwiwar mutane da su dinga shiga ayyukan da mutane ke yi don samun damar mu'amala da su sosai. Ta bayar da shawara da cewa "Za ku iya hada kungiya, kulob, kan wani abu da kuke da shawa'ar yi, ku samu sabon wasan yi don nishadi," inda ta kara da cewa "Yin sallama ga makota ko zuwa kananan kantinan unguwarku" na taimakawa sosai. Shiga ayyukan sa kai ma na taimakawa sosai, na taimakawa wajen rage kebance kai daga jama'a. Dabarar taimakawa makoci ko wani daban "na taimakawa kwakwalwa wajen jin tana tare da jama'a." Social isolation is linked to increased risk of strokes, cardiovascular disease, anxiety, depression and dementia. If you’re feeling lonely, here are some things you can do to feel better and for your health #PowerofConnection — World Health Organization (WHO) (@WHO) November 15, 2023 A yayin da duniya ke jiran shawarwarin Hukumar Magance Kadaici, akwai bukatar a dauki matakan da aka tabbatar za su taimaka. Taimako kan halin da ƙwaƙwalwar mutane ke ciki ta hanyar magani da bayar da shawarwari na da muhimmanci, kuma mutane kar su ji kunyar neman wannan taimako. Samar da duniya mai karancin kadaici Akwai bukatar a saukaka tabbatuwar hanyoyin da dabarun da za a yi amfani da su don taimakawa masu fama da matsalar kadaici da kebantuwa daga jama'a. "Duba da tasiri da illolin da kadaici da kebance kai ke da shi kan lafiya da al'umma, ya zama dole mu yi duk mai yiwuwa wajen sake gina katangar hada al'umma da za a yi amfani da ita wajen magance matsalolin lafiya, kamar shan taba sigari, kiba da zautuwa wajen amfani da wani abu," in ji Dr Vivek Murthy, daya daga cikin shugabannin hukumar. "Tare za mu iya gina duniya mai karancin kadaici, cikakkiyar lafiya da jajircewa."