Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Yadda 'dan daba ya caka' wa limami wuka yana tsaka da alwala a Kano

Ana zargin matashin da caka wa limamin wuka sakamakon nasihar da limamin ya yi masa kan ya daina shan wiwi a kusa da masallaci. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta wani dan kan zargin kashe wani limami saboda ya hana su shan wiwi a Kano. A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘ya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:23
Yadda 'dan daba ya caka' wa limami wuka yana tsaka da alwala a Kano
Bu haberde ne var?

Ana zargin matashin da caka wa limamin wuka sakamakon nasihar da limamin ya yi masa kan ya daina shan wiwi a kusa da masallaci. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta wani dan kan zargin kashe wani limami saboda ya hana su shan wiwi a Kano. A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘ya...

Ana zargin matashin da caka wa limamin wuka sakamakon nasihar da limamin ya yi masa kan ya daina shan wiwi a kusa da masallaci. Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta wani dan kan zargin kashe wani limami saboda ya hana su shan wiwi a Kano. A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, dan daban mai suna Yusuf Haruna dan shekara 18 wanda aka fi sani da Lagwatsani ya caka wa malamin wuka a bayansa yana tsaka da alwala. “A ranar 31 ga watan Disambar 2023 da misalin bakwai da rabi na dare, an samu rahoto daga wani Musa Yunusa da ke unguwar Jakara Kano kan cewa da misalin karfe bakwai na safe wani Yusuf Haruna ya caka wa Malam Sani Mohammed Shuaibu wuka a baya yana tsaka da alwala. “Ya caka masa wukar sakamakon ya gargade shi kan ya daina zukar tabar wiwi a kusa da masallaci,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yan sandan ta ce sakamakon haka ne malamin ya samu rauni wanda aka garzaya da shi asibitin Murtala inda likitoci suka tabbatar da ya rasu. Hukumar ‘yan sandan ta Kano ta tabbatar da cewa tana ci gaba da bincike kan wannan lamari kuma da zarar ta kammala za ta gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu. Ko a cikin watan Disambar da ya gabata sai da aka caka wa wani matashi mai suna Nafi’u wuka a Kano, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.