Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Yadda ƴan bindiga suka sace ɗalibai kusan 300 a wata makarantar firamare a Kaduna

Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun kusa 300, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu. Rahotanni daga Nijeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun sace gomman ɗalibai na wata makarantar firamare a ƙaram...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:23
Yadda ƴan bindiga suka sace ɗalibai kusan 300 a wata makarantar firamare a Kaduna
At a glance

Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun kusa 300, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu. Rahotanni daga Nijeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun sace gomman ɗalibai na wata makarantar firamare a ƙaram...

Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun kusa 300, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu. Rahotanni daga Nijeriya sun ce wasu ƴan bindiga sun sace gomman ɗalibai na wata makarantar firamare a ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a yau Alhamis. Duk da cewa ba a tabbatar da yawan ɗaliban da aka sace ba, amma mazauna garin sun ce sun kusa 300, inda da yawan yaran suka ruga daji bayan ganin dirar ƴan bindigar a cikin makarantar tasu. TRT Afirka Hausa ta yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumomi na gwamnatin jihar da na jam'ian tsaro, amma ba a same su ba. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa waɗanda suka shaida lamarin sun ce abin ya faru ne a lokacin da yaran suke halartar taro na asambili, kana daga bisani ƴan bindigan su kora ɗaliban da suka sace ɗin cikin daji. Ƴan bindiga da ke yawan kai hare-hare sun sha satar ɗalaibai a wasu jihohin arewacin Nijeriya, lamarin da yake yin mummunan tasiri a kan fannin ilimi a ƙasar.