الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Fasinjoji sun ji rauni bayan hatsarin jirgin ƙasa a layin Abuja–Kaduna

NRC ta ce wani ɓangaren jirgi ne ya bugi wanda ke gabansa kusa da tashar Asham Hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji sun ji rauni bayan wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru kusa da tashar Asham a layin Abuja zuwa Kaduna da safiyar Litinin. Babban daraktan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:23 ص
Fasinjoji sun ji rauni bayan hatsarin jirgin ƙasa a layin Abuja–Kaduna
لمحة سريعة

NRC ta ce wani ɓangaren jirgi ne ya bugi wanda ke gabansa kusa da tashar Asham Hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji sun ji rauni bayan wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru kusa da tashar Asham a layin Abuja zuwa Kaduna da safiyar Litinin. Babban daraktan...

NRC ta ce wani ɓangaren jirgi ne ya bugi wanda ke gabansa kusa da tashar Asham Hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji sun ji rauni bayan wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru kusa da tashar Asham a layin Abuja zuwa Kaduna da safiyar Litinin. Babban daraktan hukumar NRC, Kayode Opeifa, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe lokacin da wani ɓangaren jirgi ya bugi wani da ke gabansa. Ya ƙara da cewa nan take aka kai fasinjojin da suka ji rauni asibitin da ke kusa domin kula da lafiyarsu. Hukumar ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba, sannan an gaggauta kaddamar da matakan agajin gaggawa tare da tura jami’ai zuwa wurin domin kula da lamarin. NRC ta ce cibiyar bincike kan kariya ta fara bincike domin gano musabbabin hatsarin kamar yadda dokokin tsaro suka tanada. Daga baya jirgin ya isa tashar Idu da misalin ƙarfe 10:39 na safe bayan an cire ɓangaren da hatsarin ya shafa, inda ya yi jinkirin minti 38. Hukumar ta jaddada cewa tana ɗaukar batun tsaron fasinjoji da muhimmanci kuma za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kauce wa irin wannan lamari a nan gaba. Tushen labari: Newstimehub