Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi. Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wasu abubuwa a babban asibitin ƙaramar hukumar Bagudo da sanyin safiyar Talata. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansandan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:23
Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya
Em resumo

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi. Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wasu abubuwa a babban asibitin ƙaramar hukumar Bagudo da sanyin safiyar Talata. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansandan...

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi. Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wasu abubuwa a babban asibitin ƙaramar hukumar Bagudo da sanyin safiyar Talata. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman Anisma, a wata sanarwa ya ce tawagar ƙwararru ta EOD-CBRN ta isa wajen don gudanar da cikakken bincike kan halin da ake ciki a asibitin. Ya kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, amma wani gini a sashen gidajen ma'aikata na asibitin ya lalace, yayin da aka kwashe mutanen da ke cikinsa ba tare da matsala ba. Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi. Sai dai SP Usman ya ce Kwamishinan 'yansandan Jihar ya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin dominn tabbatar da zaman lafiya. 'Yansanda sun buƙaci jama'a da su kwantar da hankalinsu su guji kusantar wajen don nuna goyon baya ga ayyukan tsaro da bincike da ake gudanarwa.