الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Uwargidan shugaban Turkiyya ta jaddada muhimmancin hada kai don samar da zaman lafiya mai ɗorewa

Emine Erdogan ta ce, "Ba za a yi tsammanin samun nasarar shirin zaman lafiya ba, muddin ba a hada da mata ba, wadanda suke wani bangare ne na al'umma da kuma kawo sauyi," yayin da take jawabi a taron mata na taron diflomasiyya a Antalya. Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta jaddada...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:23 ص
Uwargidan shugaban Turkiyya ta jaddada muhimmancin hada kai don samar da zaman lafiya mai ɗorewa
لمحة سريعة

Emine Erdogan ta ce, "Ba za a yi tsammanin samun nasarar shirin zaman lafiya ba, muddin ba a hada da mata ba, wadanda suke wani bangare ne na al'umma da kuma kawo sauyi," yayin da take jawabi a taron mata na taron diflomasiyya a Antalya. Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta jaddada...

Emine Erdogan ta ce, "Ba za a yi tsammanin samun nasarar shirin zaman lafiya ba, muddin ba a hada da mata ba, wadanda suke wani bangare ne na al'umma da kuma kawo sauyi," yayin da take jawabi a taron mata na taron diflomasiyya a Antalya. Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta jaddada muhimmancin rawar da mata ke takawa wajen samun dauwamammen zaman lafiya a duniya. Da take jawabi ga matan shugabanni da mahalarta taron mata, zaman lafiya da tsaro na dandalin diflomasiyya na Antalya a ranar Asabar, Emine Erdogan ta ce: "Kada mu manta cewa dawwamammen zaman lafiya ya taso ne daga tsarin da ba a bar kowa a baya ba." "Ba za a yi tsammanin samun nasarar shirin zaman lafiya ba matukar ba a hada da mata, wadanda suke wani bangare ne na al'umma da kawo sauyi," in ji ta. "Ba za mu taba mika wuya ga wadanda ke kokarin rage tsarin dokokin kasa da kasa da kuma tsarin shari'a ba, wanda ke da daraja ake kuma samu da tsada, zuwa wata sanarwa kawai a rubuce," in ji Erdogan. Da take jaddada cewa a halin yanzu kasashen duniya na fuskantar rikice-rikice masu girman gaske ta yadda babu wata kasa guda da za ta iya tinkarar su ita kadai, ta bayyana cewa, “tushen dabi’u da cibiyoyi da suka hada mu a matsayin bil’adama ba su taba girgiza ba a tarihin baya-bayan nan. "Muna gudanar da wannan taro ba a cikin yanayi na lumana ba, sai dai abin bakin ciki, a karkashin halin yaki," in ji Uwargidan Erdogan, yayin da take magana kan yakin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza. Ta kara da cewa, "A wannan zamanin da nuna ƙyama da wariyar launin fata ke ƙara ta'azzara, rashin hakuri da kwadayi ke haifar da kiyayya, tabbatar da zaman lafiya da oda yana kara yin wahala." Israel must acknowledge that lasting peace in the region is possible only by establishing peace with Palestinians, says Palestinian FM Riyad al Maliki at Antalya Diplomacy Forum pic.twitter.com/JVLych05bc — TRT World Now (@TRTWorldNow) March 2, 2024 Isra'ila ta kaddamar da wani kazamin farmakin soji a Gaza na Falasdinu tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda Tel Aviv ta ce ya kashe mutanen da ba su kai 1,200. Akalla Falasdinawa 30,320 ne aka kashe tun daga lokacin, sannan wasu 71,533 suka jikkata, da kuma mummunar ɓarna da aka yi da ta jawo ƙarancin abinci da sauram kayan masarufi. Har ila yau Isra’ila ta kakaba wa Gaza takunkumai da yi mata ƙawanya, lamarin da ya bar al’ummarta, musamman mazauna arewacin Gaza, cikin faɗawa yanayin yunwa. US urges Israel to investigate itself after Israeli troops fired on starving Palestinians at Gaza aid site, killing 115 and wounding 760, as Israel's war on the tiny enclave enters its 148th day Follow our live coverage???? https://t.co/oV7UyzuWSL — TRT World (@trtworld) March 2, 2024 Yakin Isra'ila ya jefa kashi 85 cikin 100 na al'ummar Gaza gudun hijira a cikin mawuyacin hali sakamakon karancin abinci da ruwan sha mai tsafta da magunguna, yayin da kashi 60 cikin 100 na ababen more rayuwa na yankin suka lalace ko kuma suka lalace, a cewar MDD. Ana tuhumar Isra'ila da kisan kiyashi a kotun kasa da kasa. Wani hukuncin wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da ayyukan kisan kiyashi da kuma tabbatar da samar da agaji ga fararen hula a Gaza. Lamarin dai na ci gaba da jawo damuwa a tsakanin ƙasashen duniya, yana mai nuna bukatar gaggawa ta shiga tsakani na diflomasiyya da taimakon jinƙai a yankin da ke fama da rikici.