Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Uruguay ta lallasa Argentina da ci 2-0 a wasan neman zuwa gasar cin Kofin Duniya

Wannan ne karon farko da Argentina ta sha kashi a wasan neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026, kana rashin nasara ta farko tun bayan doke su da Saudiyya ta yi da ci 2-1 a wasan farko na gasar cin Kofin Duniya ta 2022 a Qatar. Uruguay ta kawo karshen wasanni 14 da zakarun gasar cin Kof...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:22
Uruguay ta lallasa Argentina da ci 2-0 a wasan neman zuwa gasar cin Kofin Duniya
Кратко

Wannan ne karon farko da Argentina ta sha kashi a wasan neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026, kana rashin nasara ta farko tun bayan doke su da Saudiyya ta yi da ci 2-1 a wasan farko na gasar cin Kofin Duniya ta 2022 a Qatar. Uruguay ta kawo karshen wasanni 14 da zakarun gasar cin Kof...

Wannan ne karon farko da Argentina ta sha kashi a wasan neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026, kana rashin nasara ta farko tun bayan doke su da Saudiyya ta yi da ci 2-1 a wasan farko na gasar cin Kofin Duniya ta 2022 a Qatar. Uruguay ta kawo karshen wasanni 14 da zakarun gasar cin Kofin Duniya Argentina suka buga a jere ba tare da an doke su ba inda suka tashi da ci 2-0 a ranar Alhamis. Argentina, wacce ta lashe Kofin Duniya a bara, ba ta yi rashin nasara ba tun bayan da Saudiyya ta lallasa ta da ci 2-1 a wasan farko da suka buga a gasar cin Kofin Duniya a bara a kasar Qatar. "Tun daga lokcin ba mu sake jin dadi ba," a cewar Kyaftin din Argentina Lionel Messi. "Rashin nasarar ta zama jarrabawa a gare mu, domin kungiya ce mai kwazo kuma fafatawa da su akwai wahala,'' in ji shi. Messi ya kara da cewa, "Suna da gwarazan 'yan wasa tsayayyu a tsakiyar filin, ba mu samu hanyar kwace kwallon na tsawon lokaci ba." Uruguay ce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan bayanta Ronald Araujo a minti na 41 da fara wasa, sannan dan wasan gaba na Liverpool Darwin Nunez ya samu nasarar cin kwallo a mintina 87, inda suka yi nasara a karshen wasan da aka buga a filin wasa na Bombonera da ke Buenos Aires. Wannan ne karo na farko da Lionel Messi da Argentina suka sha kashi a neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026, kana rashin nasara ta farko tun bayan doke su da Saudiyya ta yi da ci 2-1 a wasan farko na gasar cin Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.