"Tun ranar 7 ga watan Oktoba, Turkiyya ta bankaɗo ƙarairayin Isra'ila da dama, da kuma yadda wasu kafafen watsa labarai na duniya suka faɗa tarkonta na labaran ƙarya," in ji Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun. Turkiyya za ta ɗauki tsauraran matakai kan Isra'ila wadda take ƙoƙari ta hana Ankara bayar da tallafi ga Falasɗinawa, in ji Daraktan Sadarwa na ƙasar Fahrettin Altun. “Abubuwa da dama da sashenmu na watsa labarai da sauran sassa suke yi a ciki da wajen ƙasa suna tare da wannan matsaya,” kamar yadda Altun ya bayyana a shafin X a ranar Litinin. Turkiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi mayar da hankali wurin kai kayan agajin jin ƙai Falasdinu. "Tun ranar 7 ga watan Oktoba, Turkiyya ta bankaɗo ƙarairayin Isra'ila da dama, da kuma yadda wasu kafafen watsa labarai na duniya suka faɗa tarkonta na labaran ƙarya," in ji Altun. Ya ce ƙasarsu ta daɗe tana kira a yi adalci da kuma biyan buƙatun Falasɗinawa, musamman daga shekaru 20 da suka gabata da kuma lokacin da aka soma kai hare-hare na ranar 7 ga watan Oktoba. "Turkiyya ta amince da kasancewar yankin Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴancin kanta da ke da babban birninta a Gabashin Birnin Ƙudus kamar yadda iyakokin shekarar 1967 suka tanadar," in ji Altun.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Turkiyya za ta ɗauki tsattsauran mataki kan Isra'ila game da yaƙin Gaza
"Tun ranar 7 ga watan Oktoba, Turkiyya ta bankaɗo ƙarairayin Isra'ila da dama, da kuma yadda wasu kafafen watsa labarai na duniya suka faɗa tarkonta na labaran ƙarya," in ji Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun. Turkiyya za ta ɗauki tsauraran matakai kan Isra'ila wadda take ƙoƙari ta hana Ankara baya...

"Tun ranar 7 ga watan Oktoba, Turkiyya ta bankaɗo ƙarairayin Isra'ila da dama, da kuma yadda wasu kafafen watsa labarai na duniya suka faɗa tarkonta na labaran ƙarya," in ji Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun. Turkiyya za ta ɗauki tsauraran matakai kan Isra'ila wadda take ƙoƙari ta hana Ankara baya...
