Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Turkiyya ta yaba wa Iraƙi a kan haramta ƙungiyar PKK gabanin ziyarar da Erdogan zai kai Bagadaza

Majalisar Tsaron Ƙasa ta ayyana PKK a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda gabanin ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai kai Bagadaza bayan watan Ramadana, matakin da zai ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Iraƙi. Turkiyya ta yi maraba da matakin Majalisar Tsaron Iraƙi na ayyana ƙungiya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:22
Turkiyya ta yaba wa Iraƙi a kan haramta ƙungiyar PKK gabanin ziyarar da Erdogan zai kai Bagadaza
Kwa muhtasari

Majalisar Tsaron Ƙasa ta ayyana PKK a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda gabanin ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai kai Bagadaza bayan watan Ramadana, matakin da zai ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Iraƙi. Turkiyya ta yi maraba da matakin Majalisar Tsaron Iraƙi na ayyana ƙungiya...

Majalisar Tsaron Ƙasa ta ayyana PKK a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda gabanin ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai kai Bagadaza bayan watan Ramadana, matakin da zai ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Iraƙi. Turkiyya ta yi maraba da matakin Majalisar Tsaron Iraƙi na ayyana ƙungiyar ƴan ta'adda ta PKK a matsayin haramtacciya a ƙasar. Iraƙi ta sanar da matakin ne a wata sanarwar haɗin-gwiwa da ta fitar ranar Alhamis bayan taro kan sha'anin tsaro tsakanin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iraƙi Fuad Hussein tare da tawagoginsu a Bagadaza, babban birnin Iraƙi. An fitar da sanarwar ce a yayin da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yake shirin kai ziyara Iraƙi bayan watan azumin Ramadana — matakin da ake gani zai yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu. Dukkan ƙasashen sun tabbatar da cewa za a ɗauki ƙwararan matakai wajen tabbatar da cewa ziyarar da Shugaba Erdogan zai kai Iraƙi ta kasance mai cike da tarihi, in ji sanarwar. "Mun tattauna a kan batutuwa daban-daban da suka sahfi yankinmu da kuma ziyarar da za a kawo nan gaba," a cewar ministan harkokin wajen Iraƙi a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X. Hussein ya ƙara da cewa, "Mun jaddada buƙatar ganin an haɗa kai a fannonin tsaro da cinikayya da makamashi da harkokin ruwa da ilimi da dukkan abubuwan da ƙasashenmu za su mora."