Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Turkiyya ta soki Isra'ila kan gina sabbin gidaje a Tsaunukan Golan na Syria

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta soki Isra'ila bisa yadda take fada mamayar da ta yi a yankin Tsaunukan Golan, ind ata ce wannan cin iyakar wata kasa ne da kuma mamaya. Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi suka da babbar murya kan yadda Isra'ila ke fadada mamayar yankin Tsaunukan Golan,...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:22
Turkiyya ta soki Isra'ila kan gina sabbin gidaje a Tsaunukan Golan na Syria
Em resumo

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta soki Isra'ila bisa yadda take fada mamayar da ta yi a yankin Tsaunukan Golan, ind ata ce wannan cin iyakar wata kasa ne da kuma mamaya. Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi suka da babbar murya kan yadda Isra'ila ke fadada mamayar yankin Tsaunukan Golan,...

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta soki Isra'ila bisa yadda take fada mamayar da ta yi a yankin Tsaunukan Golan, ind ata ce wannan cin iyakar wata kasa ne da kuma mamaya. Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi suka da babbar murya kan yadda Isra'ila ke fadada mamayar yankin Tsaunukan Golan, wanda tun 1967 Isra'ilan ta mamayi yankin. A wata sanarwa, ma'aikatar ta kira matakin da "sabon matakin manufar Isra'ila ta fadada iyakokinta ta hanyar mamaya," inda ta bayyana damuwa kan illar da wannan mataki ka iya janyowa. Sakon sukar na Isra'ila ya yi karin haske kan abubuwan baya-bayan nan da ake yi a yankin, ciki har da sabawa Yarjejeniyar Barin Wajen ta 1974 ta hanyar shiga yankin, zuwa ga iyakokin daya tsallaken da kai hare-hare ta sama a Siriya. "Wadannan abubuwa da Isra'ia ke yi na lalala dukkan kokarin da ake yi na kawo zaman lafiya a Siriya da kuma kara ta'azzara wutar rikicin yankin," in ji ma'aikatar. Sanarwar ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya kamata wajen magance ci gaba da saba dokoki da Isra'ila ke yi tare da dakatar da matakan da suka karya doka da gwamnatin Netanyahu ta dauka. Kalaman na Turkiyya na bayyana damuwar kasashen duniya kan manufofin Isra'ila a Tsaunukan Golan, waje mai muhimmanci da ake ta tababa a kai tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da wasu hukumomin kasa da kasa ko kasashe.