Wakilin Turkiyya a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Sedat Onal zai koma matsayin jakadan ƙasar a Washington inda Mataimakin Ministan Harkokin Waje Ahmet Yildiz zai maye gurbinsa a MDD. Shugaban ƙasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan ya naɗa sabbin jakadu zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka. Saƙon da aka wallafa a jaridar gwamnatin Turkiyya a ranar Juma'a ta ce, an naɗa jakadan Turkiyya a Majalisar Ɗinkin Duniya Sedat Onal a matsayin sabon jakada a Amurka. Ahmet Yildiz, Mataimakin Ministan Harkokin Waje kuma ya zama sabon jakadan Turkiyya a Majalisar Ɗinkin Duniya. Sabbin jakadu zuwa Chile, Guinea, Vietnam da Guatemala. Kazalika an naɗa Rifat Cem ornekol a matsayin jakadan Turkiyya a Guinea, inda Ahmet Ihsan kiziltan kuma aka tura shi Chile a matsayin jakadan Turkiyya. Korhan Kemik ya zama jakadan Turkiyya a Vietnam, sai Beliz Celasin Rende da aka naɗa a matsayin jakadan Turkiyya a Guatemala. Sauran waɗanda aka miƙa sunayensu don naɗa su a matsayin jakadu sun haɗa da Mehmet Salt Uyanik zuwa Bulgaria, Gokcen Kaya zuwa Costa Rica, Semih Lutfu Turgut zuwa Sri Lanka da Ahmet Ergin zuwa Equitorial Guinea.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Turkiyya ta naɗa sabbin jakadu zuwa Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya
Wakilin Turkiyya a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Sedat Onal zai koma matsayin jakadan ƙasar a Washington inda Mataimakin Ministan Harkokin Waje Ahmet Yildiz zai maye gurbinsa a MDD. Shugaban ƙasar Turkiyya Recep tayyip Erdogan ya naɗa sabbin jakadu zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka. Saƙon d...