Turkiyya ta miƙa saƙon ta'aziyya ga ƙasar Pakistan kan mutuwar 'yan ƙasar sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a yankuna daban-daban na ƙasar. Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ƙasar Pakistan ranar Asabar sakamakon mutuwar ɗaruruwan ‘yan ƙasar a ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar. "Muna matuƙar baƙin ciki game da rasa rayukan da aka yi sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan," a cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya. Ta ƙara da cewa: "Muna addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga Pakistan." Hukumomi a Pakistan ranar Asabar sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya zarta 321.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Turkiyya ta miƙa saƙon ta'aziyya ga Pakistan kan mutuwar ɗaruruwan 'yan ƙasar a ambaliyar ruwa
Turkiyya ta miƙa saƙon ta'aziyya ga ƙasar Pakistan kan mutuwar 'yan ƙasar sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a yankuna daban-daban na ƙasar. Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ƙasar Pakistan ranar Asabar sakamakon mutuwar ɗaruruwan ‘yan ƙasar a ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar. "Muna mat...
Кратко