Sakamakon yadda Turkiyya ke fatattakar 'yan ta'addan, suna yawan ɓoyewa a arewacin Iraƙi kusa da iyakar Turkiyya domin kitsa kai hare-hare. Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'addan PKK/YPG 17 a arewacin Iraƙi da da arewacin Syria, kamar yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta tabbatar. Ma'aikatar ta bayar da rahoton cewa a ranar Lahadi an far wa 'yan ta'addan PKK 15 a yankunan Gara da Metina da kuma yankin arewacin Iraƙi. Sauran 'yan ta'addan biyu na PKK/YPG an kai musu hari ne a yankin Manbij da ke arewacin Syria. Ma'aikatar ta bayyana cewa sojojin Turkiyya za su ci gaba da aikinsu na yaƙi da 'yan ta'adda ba ƙaƙƙautawa a duk inda suke kamar yadda ma'aikatar ta bayyana. Hukumomi a Turkiyya suna amfani da kalmar "kawarwa" domin nuna cewa ko dai 'yan ta'addan da ake magana a kan su an kama su ko kuma an kashe su Aikin da Turkiyya ke yi na yaƙi da ta'addanci ya kusan kawar da 'yan ta'addan baki ɗaya a cikin ƙasar. A halin yanzu 'yan ta'addan na aiki ne daga kan iyakar ƙasar. Suna yawan ɓoyewa a arewacin Iraƙi kusa da iyakar Turkiyya, domin kitsa kai hari a Turkiyyar. A 2022, Turkiyya ta ƙaddamar da rundunar Operation Claw-Lock domin kai hari kan maɓoyar 'yan ta'addan PKK a yankunan Metina da Zap da Avasin-Basyan da ke arewacin Iraƙi. A tsawon shekara 40 da kungiyar ta yi tana ta'addanci a Turkiyya - kasar Turkiyya da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ta'addanci wacce ke da alhakin mutuwar mutum kusan 40,000 da suka hada da mata da yara har da jarirai.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Turkiyya ta kawar da 'yan ta'addan PKK/YPG 17 a arewacin Iraƙi da Syria
Sakamakon yadda Turkiyya ke fatattakar 'yan ta'addan, suna yawan ɓoyewa a arewacin Iraƙi kusa da iyakar Turkiyya domin kitsa kai hare-hare. Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'addan PKK/YPG 17 a arewacin Iraƙi da da arewacin Syria, kamar yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta tabbatar. Ma...

At a glance
Sakamakon yadda Turkiyya ke fatattakar 'yan ta'addan, suna yawan ɓoyewa a arewacin Iraƙi kusa da iyakar Turkiyya domin kitsa kai hare-hare. Jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da 'yan ta'addan PKK/YPG 17 a arewacin Iraƙi da da arewacin Syria, kamar yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya ta tabbatar. Ma...
