Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Turkiyya ta kawar da babbar jagorar 'yan ta'addar PKK a arewacin Iraki

Dakarun Turkiyya sun kama Rojda Bilen, da ake wa lakabi da Bisng Brusk, a wani farmakin yaki da ta'addanci da aka kai a kan iyaka a yankin Sulaymaniya na kasar Iraki. Dakarun leken asirin Turkiyya sun kawar da wata babbar jagorar 'yan ta'addar PKK/KCK a arewacin Iraki, in ji majiyoyin tsaro. Huku...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:22
Turkiyya ta kawar da babbar jagorar 'yan ta'addar PKK a arewacin Iraki
Bu haberde ne var?

Dakarun Turkiyya sun kama Rojda Bilen, da ake wa lakabi da Bisng Brusk, a wani farmakin yaki da ta'addanci da aka kai a kan iyaka a yankin Sulaymaniya na kasar Iraki. Dakarun leken asirin Turkiyya sun kawar da wata babbar jagorar 'yan ta'addar PKK/KCK a arewacin Iraki, in ji majiyoyin tsaro. Huku...

Dakarun Turkiyya sun kama Rojda Bilen, da ake wa lakabi da Bisng Brusk, a wani farmakin yaki da ta'addanci da aka kai a kan iyaka a yankin Sulaymaniya na kasar Iraki. Dakarun leken asirin Turkiyya sun kawar da wata babbar jagorar 'yan ta'addar PKK/KCK a arewacin Iraki, in ji majiyoyin tsaro. Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) sun kama Rojda Bilen da ake wa lakabi da Bisng Brusk, a wani farmakin yaki da ta'addanci da aka kai a kan iyaka a yankin Sulaymaniya na kasar Iraki, majiyar ta sanar da hakan a ranar Talata. Bilen ne babban jami'in kungiyar ta'addar a Sulaimaniyah, in ji majiyar da ta nemi a boye sunanta saboda rashin izinin yin magana da manema labarai. Majiyar ta kara da cewa ta shiga kungiyar ta'adda ta PKK a 2011 kuma tana jerin shudi na sunayen 'yan ta'addar da ake nema ruwa a jallo. An kasa jerin sunayen 'yan ta'addar da ake nema ruwa a jallo da kaloli biyar, inda Ja ya zama a kan gba,sai Shudi, Kore, Rawaya da Ruwan Toka, A cikin sama da shekaru 35 na ta'addancin da ta yi kan Turkiyya, ƙungiyar ta'adda ta PKK - wacce Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka sanya a jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda - ta ɗauki alhakin mutuwar sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata, yara da jarirai. YPG shi ne reshen ƙungiyar na Siriya. 'Yan ta'addar PKK na buya a arewacin Iraki ina suke kai hare-hare iyakar Turkiyya. Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar "kawarwa" don nufin an kashe ko kama dan ta'adda ko ya mia wuya