Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

MIT ta kama mutane biyu da ake zargi da aiki wa Mossad

An cafke su ne bayan wani aikin sirri mai suna “MONITUM” Hukumar leƙen asirin Turkiyya (MIT) ta kama mutane biyu da ake zargi da yin aiki wa hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad, bayan wani aikin yaƙi da leƙen asiri mai sarkakiya da aka sanya wa suna “MONITUM.” TRT Hausa Majiyoyin tsaron Turki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:22
MIT ta kama mutane biyu da ake zargi da aiki wa Mossad
Kwa muhtasari

An cafke su ne bayan wani aikin sirri mai suna “MONITUM” Hukumar leƙen asirin Turkiyya (MIT) ta kama mutane biyu da ake zargi da yin aiki wa hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad, bayan wani aikin yaƙi da leƙen asiri mai sarkakiya da aka sanya wa suna “MONITUM.” TRT Hausa Majiyoyin tsaron Turki...

An cafke su ne bayan wani aikin sirri mai suna “MONITUM” Hukumar leƙen asirin Turkiyya (MIT) ta kama mutane biyu da ake zargi da yin aiki wa hukumar leƙen asirin Isra’ila ta Mossad, bayan wani aikin yaƙi da leƙen asiri mai sarkakiya da aka sanya wa suna “MONITUM.” TRT Hausa Majiyoyin tsaron Turkiyya sun ce an kama Mehmet Budak Derya da Veysel Kerimoglu ne a wani samame na haɗin gwiwa tsakanin MIT, ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Istanbul da kuma sashen yaƙi da ta’addanci na rundunar ‘yansandan Istanbul. TRT Hausa Bincike ya nuna cewa Derya, injiniyan hakar ma’adanai, ya faɗaɗa kasuwancinsa zuwa cinikayyar ƙasa da ƙasa, lamarin da ake zargin ya jawo hankalin leƙen asirin Isra’ila, inda daga bisani aka haɗa shi da jami’an Mossad ta hanyar wani kamfani na bogi. TRT Hausa Haka kuma ana zargin wani jami’in Mossad ya nemi a ɗauki Veysel Kerimoglu aiki tare da Derya, inda aka umarce su da su riƙa bayar da rahoto kan ayyukansu da hulɗoɗinsu a wasu ƙasashe. TRT Hausa