Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Turkiyya ta kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi da ya nufo sararin samaniyarta ta kan Bahar Aswad

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce an kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi da aka gano kusa da Bahar Aswad a wani wuri mara hatsari bayan ya gaza mayar da martani ga matakan gudanarwa.a Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta ce an gano wani jirgi maras matuƙi da ba a san shi ba ya nufo sararin samaniyarta ta kan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:22
Turkiyya ta kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi da ya nufo sararin samaniyarta ta kan Bahar Aswad
Bu haberde ne var?

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce an kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi da aka gano kusa da Bahar Aswad a wani wuri mara hatsari bayan ya gaza mayar da martani ga matakan gudanarwa.a Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta ce an gano wani jirgi maras matuƙi da ba a san shi ba ya nufo sararin samaniyarta ta kan...

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce an kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi da aka gano kusa da Bahar Aswad a wani wuri mara hatsari bayan ya gaza mayar da martani ga matakan gudanarwa.a Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta ce an gano wani jirgi maras matuƙi da ba a san shi ba ya nufo sararin samaniyarta ta kan Bahar Aswad kuma an bibiye shi kamar yadda ake yi a tsare-tsaren tsaro. Domin tabbatar da tsaron sararin samaniyarta, an tayar da jiragen yaƙin F-16 waɗanda ƙawancen NATO ta samar kuma ƙasar take juya akalarsu domin wani aiki na kasancewa cikin shiri, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa ranar Litinin. Daga baya ya bayyana cewa jirgin maras matuƙin yana tafiya ne babu jagora, kuma daga baya aka kakkaɓo shi a wani wuri mara hatsari da ke da nisa daga inda mutane ke zama domin kauce wa ko wane irin hatsari, in ji sanarwar . Lamarin na zuwa ne cikin tashin hankali a yankin Bahar Aswad, inda Turkiyya ta yi gargaɗin kada a bar yaƙin da ake yi a Ukraine ya fantsama zuwa hanyar cinikayyar yankin.