Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Turkiyya ta horar da sojojin Gambia a kan sanin makamar aiki

Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a gudanar a farkon watan Mayu. Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a guda...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:22
Turkiyya ta horar da sojojin Gambia a kan sanin makamar aiki
At a glance

Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a gudanar a farkon watan Mayu. Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a guda...

Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a gudanar a farkon watan Mayu. Turkiyya ta horar da sojojin ƙasar Gambia, wadda ke shirin karɓar baƙuncin taron Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi OIC wanda za a gudanar a farkon watan Mayu. Jumullar sojojin Gambia 351 ne suka samu horon na musamman ta ɓangarori da dama a Banjul babban birnin ƙasar, daga 7 zuwa 28 ga watan Afrilu. Daga cikin horon da suka samu har da na naƙaltar yadda za su kare manyan baƙi. Jakadan Turkiyya a Gambia Fahri Turker Oba da Ministan Harkokin Tsaro na Gambia Sering Modou Njie da Shugaban Sojojin Gambia Mamat Cham da sojoji da dama sun samu halartar wannan taro. A lokacin taron, Oba ya bayyana cewa horon zai amfanar da sojojin na Gambiya kafin da kuma bayan taron. Nijei a ɗayan ɓangaren, ya gode wa Turkiyya kan irin goyon bayan da take bayarwa domin ci gaban Gambia.