Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Turkiyya ta dauki karin majinyata daga Gaza don ba su kulawa: Ministan Lafiya Koca

''Jimillar majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga Gaza ne aka kai su Turkiyya daga Masar,'' a cewar sanarwar da Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya fitar. Turkiyya ta dauki karin majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga yankin Gaza na Falasdinu daga Masar zuwa kasar, a cew...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:22
Turkiyya ta dauki karin majinyata daga Gaza don ba su kulawa: Ministan Lafiya Koca
Bu haberde ne var?

''Jimillar majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga Gaza ne aka kai su Turkiyya daga Masar,'' a cewar sanarwar da Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya fitar. Turkiyya ta dauki karin majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga yankin Gaza na Falasdinu daga Masar zuwa kasar, a cew...

''Jimillar majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga Gaza ne aka kai su Turkiyya daga Masar,'' a cewar sanarwar da Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya fitar. Turkiyya ta dauki karin majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga yankin Gaza na Falasdinu daga Masar zuwa kasar, a cewar wata sanarwa da Ministan lafiya na kasar Fahrettin Koca ya fitar. Ranar Alhamis da daddare ne wasu jirage biyu dauke da marasa lafiya da 'yan'uwansu suka sauka a Ankara babban birnin kasar. An kai jimillar marasa lafiya 85 da kuma wadanda suka jikkata daga Gaza zuwa Turkiyya daga Masar da maraice, a cewar sanarwar da ya wallafa a shafin X. "Marasa lafiyar sun samu rakiyar tawagar mutum 106, kuma majinyatan za su samu kulawa da kuma magani a kasarmu, "in ji Koca. Kawo yanzu Turkiyya ta amshi majinyata 292 da suka samu raunuka da kuma marasa lafiya daga Gaza domin ba su kulawa da kuma magani tun daga lokacin da Isra’ila ta soma kai munanan hare-hare a yankin Falasdinawa a shekarar 2023.