Hukumomin Turkiyya sun nuna cewa Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Katz ba shi da wata ƙima, ko da a cikin gwamnatin Netanyahu, wacce ta shahara da irin ta'asar da take yi wa ɗan adam Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah wadai da abin da Ministan Harkokin Isra'ila Katz ya wallafa a baya-bayannan a kafofin sada zumunta, inda ta bayyana shi a matsayin ƙarya da yunƙurin ɓata sunan Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Turkiyya. A wata sanarwa da aka fitar a gwamnatance, hukumomin Turkiyya sun nuna cewa Katz ba shi da wata ƙima, ko da a cikin gwamnatin Netanyahu, wacce ta shahara da irin ta'asar da take tafka wa bil adama, wacce kuma za ta bar mugun tabo a tarihi. Sanarwar ta ce Katz yana yunƙurin nuna cewa yana da muhimmanci ne ta hanyar neman suna a wajen masu amfani da kafofin sada zumunta a Turkiyya, a wani yunƙurin kare kujerarsa a cikn abin da ta bayyana "gungun masu kisan kiyashi." Turkiyya ta jaddada ƙudirinta na faɗar gaskiya da kare halastacciyar gwagwarmayar Falasɗinawa, duk da irin waɗannan soke-soke marasa tushe. Gwamnatin Turkiyya ta jaddada cewa za ta ci gaba da yin tsayuwar daka a goyon bayan da take bai wa Falasɗinawa da tabbatar da adalci.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Turkiyya ta caccaki kalaman Ministan Harkokin Wajen Isra'ila a matsayin wanda yake 'cike da ƙarairayi'
Hukumomin Turkiyya sun nuna cewa Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Katz ba shi da wata ƙima, ko da a cikin gwamnatin Netanyahu, wacce ta shahara da irin ta'asar da take yi wa ɗan adam Gwamnatin Turkiyya ta yi Allah wadai da abin da Ministan Harkokin Isra'ila Katz ya wallafa a baya-bayannan a kafof...