Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Turkiyya da Masar za su kara yawan jiragen sama da ke safara tsakaninsu

Turkiyya da Masar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ninka yawan jiragen da suke safara tsakanin kasashen biyu. Adadin jiragen saman da ke kai-komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu sama da ninki guda, in ji Ministan Sufuri da Gina Ƙasa na Turkiyya a ranar Alhamis. A karkashin sabuwar yarjejeni...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:22
Turkiyya da Masar za su kara yawan jiragen sama da ke safara tsakaninsu
Em resumo

Turkiyya da Masar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ninka yawan jiragen da suke safara tsakanin kasashen biyu. Adadin jiragen saman da ke kai-komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu sama da ninki guda, in ji Ministan Sufuri da Gina Ƙasa na Turkiyya a ranar Alhamis. A karkashin sabuwar yarjejeni...

Turkiyya da Masar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ninka yawan jiragen da suke safara tsakanin kasashen biyu. Adadin jiragen saman da ke kai-komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu sama da ninki guda, in ji Ministan Sufuri da Gina Ƙasa na Turkiyya a ranar Alhamis. A karkashin sabuwar yarjejeniyar, jiragen saman da ke kai komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu daga 30 zuwa 67 a cikin mako guda, in ji sanarwa ta Abdulkadir Uraloglu. A gawanar da aka yi a ranar Laraba a yayin Taron Hadin Kai na Kasashen Biyu a babban birnin Ankara na Turkiyya karkashin shugabancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi, an sanya hannu kan yarjeniyoyi a bangarorin sufurin jirgin kasa, da fasahar sadarwa da sufurin jiragen sama. Wannan ne karo na farko da shugaban kasa daga Masar ya ziyarci Turkiyya a cikin shekaru sama da 10, yunkurin wani bangare na Turkiyya na inganta alakarta da makotanta da ke gabar tekun Bahar Rum.