Carter, wanda ya yi shugabancin Amurka daga 1977 zuwa 1981, ya yi fice da shirye-shiryensa na zaman lafiya, da suka haɗa da Yarjejeniyar Camp David, wacce ta sulhunta Isra'ila da Masar. Shugaban Amurka na 39 Jimmy Carter ya mutu, kamar yadda jaridar Atlanta Journal-Constitution ta ba da rahoto. Ya mutu yana da shekara 100. Marigayin, ɗan jam'iyyar Democrat ya yi shugabanci daga Janairun 1977 zuwa Janairun 1981 bayan ya ka da shugaba mai ci ɗan jam'iyyar Republican Gerald Ford a zaɓen 1976. An fitar da Carter daga ofis bayan shekara huɗu a wani zaɓe da gagarumar nasara, yayin da masu zaɓe suka rungumi wanda ya yi takara da shi a jam'iyyar Republican Roanald Regan, wanda tsohon tauraron fina-finai ne kuma tsohon gwamnan California. Jimmy Carter shi ne shugaban Amurka da ya fi tsawon rai bayan barin ofis. A lokacin shugabancinsa na wa'adi ɗaya ne aka cim ma gagarumar yarjejeniyar Camp David tsakanin Isra'ila da Masar a 1978. Amma an fuskanci matsalolin koma bayan tattalin arziki ya, da rashin farin jininsa da kuma abin kunyar da ya faru na garkuwa da Amurkawa da Iran ta yi, wanda ya mamaye kwanaki 444 na ƙarshen wa’adinsa a ofis. A 'yan shekarun nan, Carter ya fuskanci matsalolin lafiya da yawa ciki har da sankarar fata nau’in melanoma, wacce ta yaɗu zuwa hantarsa da kwakwalwarsa. Carter ya yanke shawarar yin jinya a gida a cikin Fabrairu 2023 maimakon yin jinya a asibiti. Carter ya shefe shekaru da dama yana ayyukan jin ƙai. An ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2002 saboda "kokarin da yake yi na samar da hanyoyin warware rikice-rikice a duniya, don ciyar da dimukuraɗiyya da 'yancin ɗan’dam gaba, da kuma bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa." President Jimmy Carter was a Humanitarian, a patriot, an advocate. He and Muhammad Ali shared a long friendship, & we share in the country’s mourning the loss of this giant figure. “Our common humanity is stronger than the divisiveness of our fears & prejudices.”- Jimmy Carter pic.twitter.com/avAMEB8qCD — Muhammad Ali Center (@AliCenter) December 29, 2024
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu yana da shekara 100
Carter, wanda ya yi shugabancin Amurka daga 1977 zuwa 1981, ya yi fice da shirye-shiryensa na zaman lafiya, da suka haɗa da Yarjejeniyar Camp David, wacce ta sulhunta Isra'ila da Masar. Shugaban Amurka na 39 Jimmy Carter ya mutu, kamar yadda jaridar Atlanta Journal-Constitution ta ba da rahoto. Y...

Carter, wanda ya yi shugabancin Amurka daga 1977 zuwa 1981, ya yi fice da shirye-shiryensa na zaman lafiya, da suka haɗa da Yarjejeniyar Camp David, wacce ta sulhunta Isra'ila da Masar. Shugaban Amurka na 39 Jimmy Carter ya mutu, kamar yadda jaridar Atlanta Journal-Constitution ta ba da rahoto. Y...
