Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya Ghali Umar Na'Abba ya Rasu

Ghali ya rasu ne yana da shekara 65 a duniya bayan ya yi fama da jinya, a cewar wasu majiyoyi na kusa da shi. Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya, Ghali Umar Na'Abba, ya rasu. Ghali, wanda ya rike mukamin kakakin majalisar daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2003, ya rasu ne ranar Laraba da as...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:21
Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya Ghali Umar Na'Abba ya Rasu
Em resumo

Ghali ya rasu ne yana da shekara 65 a duniya bayan ya yi fama da jinya, a cewar wasu majiyoyi na kusa da shi. Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya, Ghali Umar Na'Abba, ya rasu. Ghali, wanda ya rike mukamin kakakin majalisar daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2003, ya rasu ne ranar Laraba da as...

Ghali ya rasu ne yana da shekara 65 a duniya bayan ya yi fama da jinya, a cewar wasu majiyoyi na kusa da shi. Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya, Ghali Umar Na'Abba, ya rasu. Ghali, wanda ya rike mukamin kakakin majalisar daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2003, ya rasu ne ranar Laraba da asuba a birnin Abuja bayan ya yi jinya, kamar yadda iyalansa suka bayyana. Sun kara da cewa nan gaba kadan za a tafi da shi birnin Kano domin yin jana'izarsa. An haifi marigayin a birnin Kan da ke Nijeriya a shekarar 1958. A lokacin da ya jagoranci majalisar wakilan Nijeriya, Ghali ya yi fafutuka wajen ganin majalisar ta samu 'yanci daga bangaren zartarwa tare da tabbatar da mutunta raba iko tsakanin bangarorin biyu. Ghali ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya samu shaidar karatun digiri kan Kimiyyar Siyasa a shekarar 1979.