Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Tsawa ta kashe mutum 24 a Indiya

Ruwan sama mai ƙarfi, wanda ya saɓa da lokacin sanyi na Gujarat, ya bai wa mutane da yawa mamaki, tare da wargaza ayyukansu. Mutum 24 ne suka mutu sakamakon faɗuwar da tsawa ta yi a kansu, yayin da wasu kimanin 23 suka samu raunuka, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a jihar Gujarat da ke...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:21
Tsawa ta kashe mutum 24 a Indiya
Kwa muhtasari

Ruwan sama mai ƙarfi, wanda ya saɓa da lokacin sanyi na Gujarat, ya bai wa mutane da yawa mamaki, tare da wargaza ayyukansu. Mutum 24 ne suka mutu sakamakon faɗuwar da tsawa ta yi a kansu, yayin da wasu kimanin 23 suka samu raunuka, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a jihar Gujarat da ke...

Ruwan sama mai ƙarfi, wanda ya saɓa da lokacin sanyi na Gujarat, ya bai wa mutane da yawa mamaki, tare da wargaza ayyukansu. Mutum 24 ne suka mutu sakamakon faɗuwar da tsawa ta yi a kansu, yayin da wasu kimanin 23 suka samu raunuka, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a jihar Gujarat da ke yammacin Indiya, cikin kwanaki biyun da suka gabata, kamar yadda jami'an gwamnati suka bayyana. An yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya tare da tsawa da ƙanƙara a ranakun Lahadi da Litinin a jihar, inda wasu wuraren suka samu ruwan sama mai yawan milimita 144 cikin sa'o'i 24, wanda ya ƙare a safiyar ranar Litinin, kamar yadda bayanan gwamnatin jihar suka nuna. Ruwan saman ya yi ɓarna sosai da lalata gidaje da kashe dabbobi a faɗin jihar. Ba a tsammaci irin wannan mamakon ruwan sama ba a Gujarat a cikin watannin hunturu, kuma ruwan saman mai ƙarfi ya zo wa mutane a ba-zata. "Za mu fara bincike nan ba da jimawa ba don tantance yawan asarar da aka yi,” in ji Ministan Noma na Gujarat, Raghavij Patel a ranar Litinin, inda ya ƙara da cewa za a biya diyya ga waɗanda abin ya shafa bisa sakamakon binciken. Recent satellite imagery (basedon 01:56am update) shows clear sky over Gujarat state and south Rajasthan. Moderate cloud over Mathya Pradesh, and intense to very intence cloud over north Madhya Maharasthra & Himachal Pradesh. pic.twitter.com/Swd8STpfbw — India Meteorological Department (@Indiametdept) November 26, 2023 Tasirin ruwan sama Hukumar kula da yanayi ta Indiya (IMD) ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama a sassan jihar a ranar Litinin Aƙalla dabbobi 40 ne kuma suka mutu a lamarin. A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Ministan Harkokin Cikin Gida Amit Shah ya ce ya yi matuƙar baƙin ciki da mace-mace. Gujarat ba ta saba da ganin bala'o'in ruwan sama ba. A watan Agustan shekarar 2020, mutum 14 ne suka mutu a jihar cikin kwanaki biyu kacal a wasu al’amura da suka shafi ruwan sama da kuma ambaliya. Yayin da ambaliyar ruwa da walƙiya ke kashe mutane da yawa a Indiya a kowace shekara, masana kimiyya sun yi gargaɗin cewa hauhawar yanayin zafi a duniya na haifar da bala'in yanayi mai tsanani.