Wilson Moleni, kwamishina na Ma'aikatar Kula da Harkokin Bala'i ta gwamnati (DoDMA), ya shaida wa 'yanjarida a babban birnin, Lilongwe, cewa mace-macen da lalacewar abubuwan more rayuwa sun faru ne a sassa daban-daban na ƙasar. Tsawa ta kashe mutane 14 a Malawi cikin makonni biyu da suka gabata, yayin da gidaje 8,000 suka lalace sakamakon mamakon ruwan sama, in ji jami'an kula da bala'i a ranar Jumma'a. Wilson Moleni, kwamishina na Ma'aikatar Kula da Harkokin Bala'i ta gwamnati (DoDMA), ya shaida wa 'yanjarida a babban birnin, Lilongwe, cewa mace-macen da lalacewar abubuwan more rayuwa sun faru ne a sassa daban-daban na ƙasar. “Amma tun da ƙasar na ci gaba da samun ruwan sama mai ƙarfi, akwai yiyuwar adadin mamatan zai ƙaru da lokaci,” in ji Moleni a ranar Jumma'a. Ya ce ƙungiyarsa na aiki "ba gajiya" don samar da tallafin jinƙai ga waɗanda ruwan sama ya sanya su rasa matsuguni a faɗin ƙasar. “Muna roƙon al'umma da su ɗauki matakan kariya yayin da ruwan sama ke ci gaba, domin hakan na iya hana ƙarin asarar rayuka,” ya ce. A bara, a wannan lokaci, aƙalla mutane takwas ne suka mutu, kuma iyalai 10,000 sun rasa matsuguni sakamakon ruwan sama mai ƙarfi. A shekarar 2023, guguwa mai suna Cyclone Freddy ta kashe dubban mutane a yankin kudu na ƙasar kuma ta tilasta miliyoyin mutane yin hijira. Ƙasar ba ta sake murmurewa daga ɓarnar tattalin arzikin da guguwar ta janyo ba. A cikin shekaru biyu da suka gabata, ƙasar na fama da matsanancin ƙarancin abinci. A watan da ya gabata, Shugaba Arthur Peter Mutharika ya ayyana halin bala'i na ƙasa a dukkan gundumomi 26 na ƙasar kuma ya nemi gaggawar tallafin jinƙai, amma a cewar DoDMA, har yanzu akwai "babban gibin kudi" don kauce wa rikicin jinƙai.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Tsawa ta kashe fiye da mutum 12 a Malawi sakamakon mamakon ruwan sama da walkiya
Wilson Moleni, kwamishina na Ma'aikatar Kula da Harkokin Bala'i ta gwamnati (DoDMA), ya shaida wa 'yanjarida a babban birnin, Lilongwe, cewa mace-macen da lalacewar abubuwan more rayuwa sun faru ne a sassa daban-daban na ƙasar. Tsawa ta kashe mutane 14 a Malawi cikin makonni biyu da suka gabata,...

Wilson Moleni, kwamishina na Ma'aikatar Kula da Harkokin Bala'i ta gwamnati (DoDMA), ya shaida wa 'yanjarida a babban birnin, Lilongwe, cewa mace-macen da lalacewar abubuwan more rayuwa sun faru ne a sassa daban-daban na ƙasar. Tsawa ta kashe mutane 14 a Malawi cikin makonni biyu da suka gabata,...
