Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike ya gabatar. Hukumar Kula da Layin Dogo ta Nijeriya, NRC ta fitar da sakamakon binciken da ta gudanar kan hatsarin da jirgin ƙsan Abuja-Kaduna ya yi a kwanaki baya. A sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Shugaban NRC, Kayode Opeifa, hukumar ta ce sakamakon binciken ya nuna cewa tsananin gudu da matuƙin ke yi da kuma rashin iya sarrafa birkin jirgin ne suka jawo faɗuwar da ya yi. NRC ta alaƙanta hakan da cewa kura-kurai ne irin na ɗan’adam. Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike ya gabatar. A ranar 26 ga watan Agustan da ya wuce ne jirgin ƙsan mai ɗauke da fasinjoji 618 ya kauce daga hanyarsa tare da faɗuwa inda har mutum 21 suka ji raunuka. Lamarin ya faru ne a garin Asham da ke kusa da Jere.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Tsananin gudu da kura-kuran matuƙi ne suka janyo faduwar jirgin kasan Abuja-Kaduna - NRC
Shugaban hukumar ya yi alkawarin cewa za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike ya gabatar. Hukumar Kula da Layin Dogo ta Nijeriya, NRC ta fitar da sakamakon binciken da ta gudanar kan hatsarin da jirgin ƙsan Abuja-Kaduna ya yi a kwanaki baya. A sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun S...