Ya yi gargaɗin kai hari kan wuraren mai idan Iran ta ci gaba da kawo tangarɗa a Mashigin Hormuz Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rundunar sojin Amurka ta kai wani babban hari a Tsibirin Kharg na Iran, yana mai cewa harin na daga cikin manyan hare-haren bam da aka taɓa kaiwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Trump ya ce harin ya lalata wuraren soji da Iran ke amfani da su a tsibirin, amma ya ƙara da cewa bai ba da umarnin lalata wuraren mai da ke wurin ba. Sai dai ya yi gargaɗin cewa idan Iran ko wani ya ci gaba da kawo tangarɗa ga zirga-zirgar jiragen ruwa ta Mashigin Hormuz, Amurka za ta iya kai hari kan wuraren mai. Tsibirin Kharg, wanda ke kusan kilomita 30 daga gabar Iran, na da matuƙar muhimmanci ga fitar da ɗanyen mai na ƙasar, domin kusan kashi 90 cikin 100 na man Iran ana fitar da shi ne ta wannan tsibiri. Masana sun ce duk wani hari a wurin na iya haifar da gagarumin tasiri ga kasuwar makamashi ta duniya. A halin yanzu, rikicin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran ya haddasa dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Hormuz, hanyar da kusan kashi ɗaya cikin biyar na man duniya da iskar gas na LNG ke bi. Trump ya kuma ce rundunar sojin ruwan Amurka za ta fara rakiyar tankokin mai da sauran jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar domin tabbatar da ci gaba da jigilar mai da kuma rage hauhawar farashin makamashi. Tushen labari: Newstimehub
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Trump ya ce Amurka ta kai babban hari a Tsibirin Kharg na Iran
Ya yi gargaɗin kai hari kan wuraren mai idan Iran ta ci gaba da kawo tangarɗa a Mashigin Hormuz Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rundunar sojin Amurka ta kai wani babban hari a Tsibirin Kharg na Iran, yana mai cewa harin na daga cikin manyan hare-haren bam da aka taɓa kaiwa a yankin...

Bu haberde ne var?
Ya yi gargaɗin kai hari kan wuraren mai idan Iran ta ci gaba da kawo tangarɗa a Mashigin Hormuz Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rundunar sojin Amurka ta kai wani babban hari a Tsibirin Kharg na Iran, yana mai cewa harin na daga cikin manyan hare-haren bam da aka taɓa kaiwa a yankin...
