Barkwanci Kan Epstein Ya Fusata Shugaban Amurka Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shigar da ƙara a kotu kan mai gabatar da Gasar Grammy ta 68, Trevor Noah, bayan barkwancin da ya yi a wajen bikin wanda ya ambaci Trump da kuma marigayi Jeffrey Epstein da aka tabbatar da laifin cin zarafin mata ta hanyar lalata. TRT Hausa Trevor Noah, dan Afirka ta Kudu kuma mai gabatar da Grammys, ya yi barkwanci ne yayin taya Billie Eilish murna kan lashe Grammy na Wakar Shekara, inda ya kwatanta nasarar da sha’awar Trump kan Greenland, sannan ya danganta Epstein da batun neman sabon tsibiri, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce. TRT Hausa Martanin barkwancin ya fusata Trump, wanda ya mayar da martani ta shafinsa na Truth Social, inda ya soki Gasar Grammy tare da musanta duk wata alaƙa da Epstein, yana mai cewa bai taɓa zuwa tsibirinsa ba. TRT Hausa Trump ya bayyana cewa maganganun Trevor Noah ƙarya ne, yana mai cewa zai tura lauyoyinsa domin ɗaukar matakin shari’a a kansa. TRT Hausa Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da aka saki takardu da dama da suka ambaci sunayen fitattun mutane masu ƙarfi a duniya, ciki har da Donald Trump, Bill Clinton, Bill Gates da wasu manyan mutane, lamarin da ke ci gaba da tayar da muhawara a duniya. TRT Hausa
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Trump Ya Yi Barazanar Kai Ƙara Kan Mai Gabatar da Grammy
Barkwanci Kan Epstein Ya Fusata Shugaban Amurka Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shigar da ƙara a kotu kan mai gabatar da Gasar Grammy ta 68, Trevor Noah, bayan barkwancin da ya yi a wajen bikin wanda ya ambaci Trump da kuma marigayi Jeffrey Epstein da aka tabbatar da laifin cin zaraf...

Em resumo
Barkwanci Kan Epstein Ya Fusata Shugaban Amurka Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar shigar da ƙara a kotu kan mai gabatar da Gasar Grammy ta 68, Trevor Noah, bayan barkwancin da ya yi a wajen bikin wanda ya ambaci Trump da kuma marigayi Jeffrey Epstein da aka tabbatar da laifin cin zaraf...
