Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Tinubu zai rage yawan ma’aikatun gwamnatin tarayyar Nijeriya

Wata sanarwa da fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a yau Litinin ta ce za ta kuma yi hakan ta hanyar rage yawan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar ƙasar. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa ta hanyar amfani da shawarwarin Rahoton Or...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:21
Tinubu zai rage yawan ma’aikatun gwamnatin tarayyar Nijeriya
Кратко

Wata sanarwa da fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a yau Litinin ta ce za ta kuma yi hakan ta hanyar rage yawan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar ƙasar. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa ta hanyar amfani da shawarwarin Rahoton Or...

Wata sanarwa da fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a yau Litinin ta ce za ta kuma yi hakan ta hanyar rage yawan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar ƙasar. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa zai rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa ta hanyar amfani da shawarwarin Rahoton Oronsaye. Wata sanarwa da fadar Shugaban Ƙasar ta fitar a yau Litinin ta ce za ta kuma yi hakan ta hanyar rage yawan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar ƙasar. Shekaru 12 bayan da kwamitin Steve Oronsaye ya gabatar da rahotonsa na sake fasali da kuma daidaita ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da wani rahoton gwamnati da ya ba da bayanai da shawarwari kan batun da aka fitar bayan shekaru biyu, Shugaba Tinubu da Majalisar Zartarwa ta tarayya a yau sun yanke shawarar aiwatar da rahoton," in ji sanarwar da Bayo Onanuga, mai taimaka wa Shugaban Ƙasar kan watsa labarai ya wallafa a shafinsa na X. Sanarwar ta ƙara da cewa za a haɗe hukumomi da dama domin shimfida hanyar samar da gwamnati mai sassaucin ra'ayi.