Shugaban Nijeriya ya yi Allah wadai da harin ‘yan ta’adda a Kaiama, ya bayar da umarnin ɗaukar matakin gaggawa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura wata bataliya ta soji zuwa ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, bayan da ‘yan ta’adda suka kashe sama da mutum 160 a ƙauyen Worro da kewaye. TRT Hausa Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce rundunar sojin za ta yi aiki ne ƙarƙashin dakaru na musamman na Operation Savannah Shield domin daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da kuma kare al’ummomin da ba su da kariya. TRT Hausa Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin “ragwanci da dabbanci,” inda ya ce maharan marasa tausayi ne da suka kai hari kan fararen hula saboda sun ƙi karɓar wata aƙida mai tsattsauran ra’ayi. TRT Hausa Shugaban ya bayyana cewa abin yabawa ne yadda mutanen garin, duk da kasancewarsu Musulmai, suka ƙi yarda a tilasta musu wata aƙida da ke fifita tashin hankali maimakon zaman lafiya da tattaunawa. TRT Hausa Ya kuma yi kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin ba da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. TRT Hausa Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnatin jihar Kwara, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan. TRT Hausa Rahotanni daga Nijeriya sun ce an kashe fiye da mutum 160 a daren Talata bayan hare-haren da wasu masu iƙirarin jihadi suka kai ƙauyukan Woro da Nuku a Kaiama, yayin da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya tabbatar da mutuwar mutum 75. TRT Hausa Gwamnan ya ce an kashe mutanen ne saboda sun ƙi miƙa wuya ga masu tsattsauran ra’ayi da ke ƙoƙarin yada wata sabuwar aƙida, inda ake zargin maharan sun fito ne daga gandun dajin Kainji da ke jihar Neja. TRT Hausa Jihar Kwara na daga cikin jihohin da ke fuskantar barazanar ‘yan ta’adda a Nijeriya, bayan jerin hare-hare da suka shafi fararen hula da wuraren ibada a ‘yan lokutan nan. TRT Hausa
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Tinubu Ya Tura Bataliya ta Soji Bayan Kisan Sama da Mutane 160 a Jihar Kwara
Shugaban Nijeriya ya yi Allah wadai da harin ‘yan ta’adda a Kaiama, ya bayar da umarnin ɗaukar matakin gaggawa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura wata bataliya ta soji zuwa ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, bayan da ‘yan ta’adda suka kashe sama da mutum 160 a ƙauyen...

Em resumo
Shugaban Nijeriya ya yi Allah wadai da harin ‘yan ta’adda a Kaiama, ya bayar da umarnin ɗaukar matakin gaggawa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura wata bataliya ta soji zuwa ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, bayan da ‘yan ta’adda suka kashe sama da mutum 160 a ƙauyen...
