Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu 'yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12

Biyan bashin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Super Eagles ke shirin wasa a gasar AFCON wadda za a yi a Ivory Coast. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin wasannin Nijeriya suke bi, daga ciki har da kungiyar Super Eagles. Daga cikin bash...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:21
Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu 'yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12
Bu haberde ne var?

Biyan bashin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Super Eagles ke shirin wasa a gasar AFCON wadda za a yi a Ivory Coast. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin wasannin Nijeriya suke bi, daga ciki har da kungiyar Super Eagles. Daga cikin bash...

Biyan bashin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Super Eagles ke shirin wasa a gasar AFCON wadda za a yi a Ivory Coast. Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin wasannin Nijeriya suke bi, daga ciki har da kungiyar Super Eagles. Daga cikin bashin da za a biya, har da kudaden da manyan kociya ke bi na albashinsu wanda ya kai watanni 15. Haka kuma akwai alawus-alawus da kuma alkawura da aka yi wa manyan ‘yan wasa maza da mata da ‘yan kasa da shekara 20. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles ke shirin soma wasa a gasar AFCON wadda za a fara a cikin watan nan na Janairu. Tun a bara sai dai kungiyar ta Super Eagles ta yi barazanar kin buga gasar ta AFCON kan kin biyanta hakkokinta. Masu sharhi dai sun sha danganta rashin rashin karsashi da a wasu lokuta ‘yan wasan na Nijeriya ke nunawa a wasannin nasu da rashin biyansu hakkokinsu da suka dace wanda hakan ke kara sanyaya musu gwiwa.