Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Tinubu na son Majalisar Dokokin Nijeriya ta amince ya karbo bashin N1.77tn

Idan har majalisar ta amince, to za a yi amfani da bashin wajen cike giɓin kasafin kudin kasar na 2023 na naira tiriliyan 9.7. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dokokin neman ta amince a karɓo bashin naira tiriliyan 1.767 a matsayin shirin dokar kasafin kudi na 2024 na sabon ra...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:21
Tinubu na son Majalisar Dokokin Nijeriya ta amince ya karbo bashin N1.77tn
Kwa muhtasari

Idan har majalisar ta amince, to za a yi amfani da bashin wajen cike giɓin kasafin kudin kasar na 2023 na naira tiriliyan 9.7. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dokokin neman ta amince a karɓo bashin naira tiriliyan 1.767 a matsayin shirin dokar kasafin kudi na 2024 na sabon ra...

Idan har majalisar ta amince, to za a yi amfani da bashin wajen cike giɓin kasafin kudin kasar na 2023 na naira tiriliyan 9.7. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dokokin neman ta amince a karɓo bashin naira tiriliyan 1.767 a matsayin shirin dokar kasafin kudi na 2024 na sabon rancen da za a ciyo daga waje. Idan har majalisar ta amince, to za a yi amfani da bashin wajen cike giɓin kasafin kudin kasar na 2023 na naira tiriliyan 9.7. Shugaban Majalisar Wakilai ne ya karanta buƙatar Shugaban Ƙasar a yayin zaman majalisar a ranar Talata. Shugaban Ƙasar ya kuma miƙa wa majalisar ƙudurorin samar da Shirin Bayar da Tallafi na Ƙasa da kuma na MTEF/ FSP 2025- 2027, don aiwatar da shirye-shiryen gwamnatin tarayya na tallafa wa mutane. Wannnan na zuwa ne a yayin da Babban Bankin Nijeriya CBN a kwanan nan ya ce Gwamnatin Tarayya ta kashe dala biliyan 3.58 don biyan bashin ƙasashen waje da ake bin ƙasar a watanni taran farko na shekarar 2024.