Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Tawagar IMF ta kai ziyara Nijar domin ba da taimako na ƙwararru

A watan Mayun da ya gabata wata tawagar IMF ta gana da Firaministan Jamhuriyar Nijar game da garambawul kan tattalin arzikin ƙasar. Firaminista kuma Ministan Kuɗi na Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Asusun Ba Da Lamuni na IMF da ta kai ziyarar aikin ƙasar Nijar r...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:21
Tawagar IMF ta kai ziyara Nijar domin ba da taimako na ƙwararru
De un vistazo

A watan Mayun da ya gabata wata tawagar IMF ta gana da Firaministan Jamhuriyar Nijar game da garambawul kan tattalin arzikin ƙasar. Firaminista kuma Ministan Kuɗi na Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Asusun Ba Da Lamuni na IMF da ta kai ziyarar aikin ƙasar Nijar r...

A watan Mayun da ya gabata wata tawagar IMF ta gana da Firaministan Jamhuriyar Nijar game da garambawul kan tattalin arzikin ƙasar. Firaminista kuma Ministan Kuɗi na Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Asusun Ba Da Lamuni na IMF da ta kai ziyarar aikin ƙasar Nijar ranar Laraba domin tattaunawa kan harkokin kuɗi da tsimi da tanadi. Tawagar ta ƙwararru ta kai ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin Ms. HA VU, babbar masaniyar tattalin arziki a ɓangaren kuɗi da haraji na asusun a IMF. Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar, ANP ya ambato wata sanarwa na cewa, "Nijar a matsayinta na mamba a Asusun Ba Da Lamuni na IMF, ta nemi wannan taimakon na ƙwararru daga IMF domin inganta da kuma ƙarfafa ayyukan gwamnati."