Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Taurarin Afirka na cikin jerin sunayen ƙyautar 'BET Hip Hop Awards' na 2024

Ƙyautar BET Hip Hop ta biyo bayan nasarar da aka samu kwanan nan na lambobin yabo na BET, inda taurarun Afirka a fannin wakoƙi suka mamaye rukunai da dama. Shirin karrama tauraru na BET ya sanar da sunayen mawaƙan da za a zaɓa domin samun lambar yabo a fagen salon wakoƙin Hip Hop na wannan shekar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:21
Taurarin Afirka na cikin jerin sunayen ƙyautar 'BET Hip Hop Awards' na 2024
Кратко

Ƙyautar BET Hip Hop ta biyo bayan nasarar da aka samu kwanan nan na lambobin yabo na BET, inda taurarun Afirka a fannin wakoƙi suka mamaye rukunai da dama. Shirin karrama tauraru na BET ya sanar da sunayen mawaƙan da za a zaɓa domin samun lambar yabo a fagen salon wakoƙin Hip Hop na wannan shekar...

Ƙyautar BET Hip Hop ta biyo bayan nasarar da aka samu kwanan nan na lambobin yabo na BET, inda taurarun Afirka a fannin wakoƙi suka mamaye rukunai da dama. Shirin karrama tauraru na BET ya sanar da sunayen mawaƙan da za a zaɓa domin samun lambar yabo a fagen salon wakoƙin Hip Hop na wannan shekara, kuma a bana taurarin Afirka ne suka mamaye rukunin matakai da dama da aka ware. Daga cikin fitattun 'yan Afirka da aka zaɓa, akwai Burna Boy wanda ake sa ran zai lashe ƙyautar tauraron mawaƙi da ya fi kowa iya rera waƙa kai tsaye. Tauraron mawaƙin ɗan Nijeriya zai fafata da fitattun manyan mawaƙa da duniya ta san da zamansu kamar Kendrick Lamar da Nicki Minaj da Travis Scott da dai sauransu. A fagen ƙyautar 'Best Flow category' a duniya ODUMODUBLVCK yana kan gaba, ɗan gambarar mawaƙin daga Nijeriya zai fafata da mawaƙan Afirka ta Kudu biyu wato Maglera Doe Boy da Blxckie, da kuma wasu daga Birtaniya Ghetts da Stefflon Don, a cikin wannan rukuni mai matukar zafi. Ƙyautar BET Hip Hop ta biyo bayan nasarar da aka samu kwanan nan na lambobin yabo na BET, inda taurarun Afirka a fannin wakoƙi suka mamaye rukunai da dama. Tyla da Makhadzi daga ƙasar Afirka ta Kudu da Tems daga Nijeriya, duk sun karbi kyautuka masu daraja. Taron ba da ƙyautar BET Hip Hop na 2024 zai gudana ne a birnin Las Vegas a karon farko a ranar 15 ga Oktoba. Shugaba kuma wanda ya assasa BET Scott Mills ya nuna farin cikinsa game da kawo shirin zuwa birni wanda aka san shi da annashuwa da karshashi da kuma tarihi a fannin nishaɗi.