الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Taron diflomasiyya na Antalya ya bankaɗo munafuncin manyan ƙasashen duniya: Fidan

Ana gudanar da muhimmiyar tattaunawa da zummar ganin an tsagaita wuta a Gaza kafin soma azumin watan Ramadan, a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan. Mahalarta taro kan diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum (ADF) sun bayyana baki-biyu da manyan ƙasashen duniya suke yi game da batu...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:21 ص
Taron diflomasiyya na Antalya ya bankaɗo munafuncin manyan ƙasashen duniya: Fidan
لمحة سريعة

Ana gudanar da muhimmiyar tattaunawa da zummar ganin an tsagaita wuta a Gaza kafin soma azumin watan Ramadan, a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan. Mahalarta taro kan diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum (ADF) sun bayyana baki-biyu da manyan ƙasashen duniya suke yi game da batu...

Ana gudanar da muhimmiyar tattaunawa da zummar ganin an tsagaita wuta a Gaza kafin soma azumin watan Ramadan, a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan. Mahalarta taro kan diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum (ADF) sun bayyana baki-biyu da manyan ƙasashen duniya suke yi game da batutuwa daban-daban, tare da yin watsi da dokokin ƙasashen duniya, a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan. Da yake jawabi na rufe taron nan ADF ranar Lahadi, wanda aka gudanar a kudancin Turkiyya, Hakan Fidan ya ce ana gudanar da muhimmiyar tattaunawa da zummar ganin an tsagaita wuta a Gaza kafin soma azumin watan Ramadan. Ƙarni na 21 ya zama zamanin rikice-rikice —Shugaban ƙasar Turkiyya Erdogan Ya kara da cewa Turkiyya tana goyon bayan yanayin da zai kawar da tsarin ƙasashen duniya a kan Gaza domin a samar da mafita a yankin. Fatan tattaunawa don tsagaita wuta a Ukraine Ya ƙara da cewa Turkiyya tana fata a ci gaba da tattaunawa domin tsagaita wuta a Ukraine. "Ya kamata a soma tattaunawa domin tsagaita wuta (a Ukraine). Hakan ba ya nufin a yarda da mamaya, amma ya kamata a tattauna game da ƴancin gashin kan ƙasa daban, da kuma batun tsagaita wuta shi ma daban," in ji Fidan. Haka kuma Fidan ya ce ana shirin tafiya Amurka a makon gobe bayan ya samu gayyata daga Sakataren Harkokin Wajen ƙasar Antony Blinken don yi taro na musamman.