Wata tankar mai wadda ke cike da man fetur ta yi bindiga a ranar Asabar a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke a Jihar Neja. Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗin da ke cikin tankar. Gomman mutane ne suka ƙone ƙurmus sakamakon fashewar da tankar ta yi wasu kuma sun jikkata, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar ya ruwaito. Gwamnan Jihar Neja Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa a sanarwar da sakataren watsa labaran Bologi Ibrahim ya fitar. Ana yawan samun fashewar tankar mai bayan ta yi hatsari a Nijeriya inda jama'a da dama da ke zuwa kwalfar man fetur ke mutuwa. Ko a kwanakin baya sai da fiye da mutum 100 suka rasu a gobarar tankar mai a Jigawa.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Tankar mai ta yi bindiga kan hanyar Kaduna-Abuja a Nijeriya
Wata tankar mai wadda ke cike da man fetur ta yi bindiga a ranar Asabar a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke a Jihar Neja. Rahotanni sun ce tankar man ta yi bindiga ne bayan wani ƙaramin hatsari da ta samu, inda jama’ar da ke kusa da wurin suka je kwalfar fetur ɗ...

At a glance