Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Ta'addanci ba shi da wurin zama a Turkiyya da yankunanta: Erdogan

Dukkan ƙungiyoyin ta'addanci, da suka haɗa da PKK, FETO, Daesh, da DHKP-C, "maƙiya" ne na al'ummar Turkiyya, a cewar shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa ta kakkaɓe duk wata barazanar ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba kawai a ƙasar ba, har...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:21
Ta'addanci ba shi da wurin zama a Turkiyya da yankunanta: Erdogan
De un vistazo

Dukkan ƙungiyoyin ta'addanci, da suka haɗa da PKK, FETO, Daesh, da DHKP-C, "maƙiya" ne na al'ummar Turkiyya, a cewar shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa ta kakkaɓe duk wata barazanar ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba kawai a ƙasar ba, har...

Dukkan ƙungiyoyin ta'addanci, da suka haɗa da PKK, FETO, Daesh, da DHKP-C, "maƙiya" ne na al'ummar Turkiyya, a cewar shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan. Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa ta kakkaɓe duk wata barazanar ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba kawai a ƙasar ba, har ma da duka yankin a nan gaba. "A shirye muke mu nuna cewa ta'addanci ba shi da mazauni a makomar Turkiyya da ma yankinta. Zaɓen da aka gudanar na baya-bayan na ya ƙara mana ƙaimi," in ji Erdogan yayin da yake jawabi a wani taron buɗa-baki da ya gudanar a shugabannin jami'an tsaro a Ankara ranar Laraba. Ya jaddada cewa ta'addanci lamari ne da babu ruwansa da ra'ayinka na siyasa don haka ya kama a ɗauke shi da muhimmanci. Erdogan ya ce dukkan ƙungiyoyin ta'addanci, da suka haɗa da PKK, FETO, Daesh, da DHKP-C, "maƙiyan" al'ummar Turkiyya ne. A kusan shekaru 40 da PKK - wadda Turkiyya da Amurka da Tarayya Turai suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci - ta kwashe tana yaƙi da Turkiyya ta kashe mutum sama da 40,000, ciki har da mata da ƙananan yara da jarirai. FETO da shugabanta da ke zaune a Amurka Fetullah Gulen sun kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba na ranar 15 ga watan Yulin 2016 a Turkiyya, inda aka kashe mutum 252 sannan aka jikkata 2,734.