Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Sudan ta yi wa jakadanta na Kenya kiranye bayan ziyarar Dagalo

Sudan ta yi wa jakadanta da ke Kenya kiranye bayan da shugaban kasar William Ruto ya karbi bakwancin shugaban rundunar RSF Janar Mohamed Dagalo a ranar Laraba. Sudan ta kira jakadanta daga Nairobi zuwa gida a wani mataki na nuna rashin jin dadinta game da taron da shugaban kasar Kenya Willian Rut...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:21
Sudan ta yi wa jakadanta na Kenya kiranye bayan ziyarar Dagalo
A taƙaice

Sudan ta yi wa jakadanta da ke Kenya kiranye bayan da shugaban kasar William Ruto ya karbi bakwancin shugaban rundunar RSF Janar Mohamed Dagalo a ranar Laraba. Sudan ta kira jakadanta daga Nairobi zuwa gida a wani mataki na nuna rashin jin dadinta game da taron da shugaban kasar Kenya Willian Rut...

Sudan ta yi wa jakadanta da ke Kenya kiranye bayan da shugaban kasar William Ruto ya karbi bakwancin shugaban rundunar RSF Janar Mohamed Dagalo a ranar Laraba. Sudan ta kira jakadanta daga Nairobi zuwa gida a wani mataki na nuna rashin jin dadinta game da taron da shugaban kasar Kenya Willian Ruto ya shirya da shugaban dakarun RSF Mohamed Dagalo, a cewar mukaddashin ministan harkokin wajen Sudan . Dagalo, wanda dakarunsa ke yaki da rundunar sojin Sudan karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan tun a watan Afrilu shekarar 2023, yana rangadi a manyan biranen kasashen Afirka a ziyararsa ta farko zuwa kasashen ketare tun da rikicin ya barke. Tuni dai ya ziyarci kasashen Uganda da Habasha da Djibouti da kuma Kenya, kuma a halin yanzu yana Afrika ta Kudu, lamarin da ke kara fusata Burhan. A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na SUNA ya fitar a ranar Alhamis, mukaddashin ministan harkokin wajen Sudan Ali al-Sadiq ya ce an kira jakadan ne domin ''tattaunawa da kuma nuna adawa bisa tarba da liyafar da gwamnatin Kenya ta shirya.'' Tsamin dangantaka Ya ce tattaunawar da za a yi "za ta kunshi yiwuwar sakamakon dangantakar Sudan da Kenya." A tsawon watanni dangantaka tsakanin Burhan da gwamnatin Kenya ta yi tsami, kasancewar Nairobi ta nemi hanyoyin sadarwa da Dagalo don ta samu damar shiga tsakani a rikicin. Yakin Sudan ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 12,190, a cewar alkaluman cibiyar da ke tattara bayanai kan yaki sannan ya tilasta wa mutane sama da miliyan bakwai barin gidajensu a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya MDD.