Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kwale-kwale Ya Nutse a Kogin Nilu, Mutum 21 Sun Mutu a Sudan

Hatsarin ya faru ne a arewacin ƙasar yayin tsallaka kogin. Aƙalla mutum 21 sun mutu bayan wani kwale-kwale ya nutse a Kogin Nilu a arewacin Sudan, kamar yadda gwamnatin jihar da ganau suka bayyana. TRT Hausa Gwamnatin Jihar River Nile ta ce an gano gawarwaki 21 tare da bayyana sunayensu, yayin da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:21
Kwale-kwale Ya Nutse a Kogin Nilu, Mutum 21 Sun Mutu a Sudan
At a glance

Hatsarin ya faru ne a arewacin ƙasar yayin tsallaka kogin. Aƙalla mutum 21 sun mutu bayan wani kwale-kwale ya nutse a Kogin Nilu a arewacin Sudan, kamar yadda gwamnatin jihar da ganau suka bayyana. TRT Hausa Gwamnatin Jihar River Nile ta ce an gano gawarwaki 21 tare da bayyana sunayensu, yayin da...

Hatsarin ya faru ne a arewacin ƙasar yayin tsallaka kogin. Aƙalla mutum 21 sun mutu bayan wani kwale-kwale ya nutse a Kogin Nilu a arewacin Sudan, kamar yadda gwamnatin jihar da ganau suka bayyana. TRT Hausa Gwamnatin Jihar River Nile ta ce an gano gawarwaki 21 tare da bayyana sunayensu, yayin da ta gargaɗi cewa har yanzu ba a san inda wasu daga cikin fasinjojin suke ba, a cewar rahoton kamfanin dillancin labaran AFP. TRT Hausa Rahotanni sun ce kwale-kwalen na tsallaka Kogin Nilu ne tsakanin ƙauyukan Tayba al-Khawad da Deim al-Qarai lokacin da hatsarin ya faru, amma sanarwar gwamnati ba ta bayyana musabbabin lamarin ba. TRT Hausa Ganau sun shaida wa AFP cewa kwale-kwalen na ɗauke da kusan mutum 30 a lokacin da ya nutse. TRT Hausa Ƙungiyar Sudanese Doctors Network ta bayyana cewa mutane shida daga cikin fasinjojin sun tsira, tana mai alaƙanta hatsarin da raunin sufirin ruwa da kuma rashin kayan tsaro da hanyoyin ceto a farkon faruwar lamarin. TRT Hausa Ƙungiyar ta kuma ce da dama daga cikin ‘yan Sudan na dogaro da sufirin ruwa ta amfani da kwale-kwale masu ƙaramin inji, a daidai lokacin da yaƙin cikin gida ke ƙara lalata ababen more rayuwa da hidimomin jama’a a ƙasar. TRT Hausa